Mahaifin Dalibi Ya Yi wa Malamar Makarantarsu Dukan Tsiya har Lahira
- Wata malamar makaranta ta mutu bayan an zargi mahaifin wani ɗalibi da dukan ta har lahira wanda ya tayar da hankula
- Rahotanni sun ce rikicin ya fara ne bayan malamar ta hukunta wani ɗalibi, lamarin da ya jawo mahaifinsa ya kai mata hari mai muni
- Lamarin ya tayar da hankalin jama'a, yayin da ake kira ga hukumomi su gudanar da bincike tare da tabbatar da an yi wa malamar adalci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lokoja, Kogi - Malamar makaranta ta rasu bayan an yi zargin cewa mahaifin wani ɗalibi ya lakada mata dukan tsiya.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa mutumin ya yi mata duka har ta sheka lahira a yankin Okpo na ƙaramar hukumar Olamaboro a Kogi.

Source: Original
Rahotanni daga Zagazola Makama sun tabbatar da wannan mummunan lamari wanda ya tayar da hankulan alumma.
Hukunta dalibi ya yi sanadiyar ran malamar makaranta
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan malamar ta hukunta ɗalibin saboda aikata laifi.
Hakan ya haddasa sa-in-sa tsakaninta da mahaifin yaron, wanda ake zargin ya rikide zuwa tashin hankali har ta mutu, lamarin da ya tayar da hankulan al'ummar yankin gaba daya.
Wannan lamari mai tayar da hankali ya jawo fushin jama'a tare da ƙara nuna damuwa kan tsaron malamai da rashin mutunta masu koyarwa a al'umma.
Ana sauraron hukumomi domin daukar mataki
Mutuwar malamar ta haifar da tambayoyi kan makomar ilimi da kariyar malamai, domin idan malamai ba za su iya ladabtar da ɗalibai ba saboda tsoron rasa rayukansu, tsarin ilimi zai shiga babban haɗari.
Ana sa ran hukumomi za su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da hannu domin a yi wa marigayiyar adalci, kamar yadda Daily Post ta ce.
An zanga-zanga kan dukan dalibi
A kwanakin baya ma, mun kawo muku rahoton yadda wani malami ya yi wa ɗalibinsa dukan kawo wuka har ya bakunci lahira sanadiyar dukan da aka yi masa.
Al'ummar garin Oko Afo da ke jihar Legas sun shiga tashin hankali yayin da wani abun bakin ciki ya faru a daya daga cikin makarantun yankin.
An rahoto cewa wani malamin makarantar mai suna Oluwale, ya yi wa daya daga cikin dalibansa, David Babadipo duka har sai da ya bakunci lahira.
Wannan al'amari ya haddasa tashin hankali, inda dalibai suka gudanar da zanga-zanga kan mutuwar abokin karatunsu.
Dalibai sun yi wa malami dukan tsiya
A baya, an ji cewa jami'an 'yan sandan jihar Ogun sun kama wasu matasa dalibai da ake zargin sun daka malaminsu a makaranta wanda ya tayar da hankula.
Daliban su 10 ana zarginsu da cin zarafin malamin bayan ya kama daya daga cikinsu ya na satar amsa wanda hukumomi a makarantar suka haramta gaba ɗaya.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar a wancan lokaci, Omotola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce an kwamushe daliban.
Asali: Legit.ng

