Kisan miji: Za a fara sauraron shari’an Maryam Sanda a yau
A yau aka za a fara sauraron shari’an Maryam Sanda, matar da yan sanda suka zarga da kashe mijinta, Bilyamin Bello.
Ana sanya ran yan sanda zasu kira shaidansu na farko.
Kotun da ake shari’an na Jabi ta daga sauraron al’amarin zuwa ranar 19 ga watan Maris yayinda aka bada belin Maryam Sanda.
A ranar 7 ga watan Maris, kotun ta ba da belin wacce ake zargin bayan sun bukaci haka a karo na biyar.
KU KARANTA KUMA: Ko sama ko kasa: An nemi shaida an rasa a wajen sauraran karar Maryam Sanda
Mai shari’a Yusuf Halilu, wanda yaki amincewa da bayar da belinta har sau hudu, ya bayyana cewa kotun ta gamsu da dalilin rashin lafiya da aka gabatar akan Maryam.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng