Sanatar da ta sha mari ta yi magana

Sanatar da ta sha mari ta yi magana

Rahotanni sun kawo cewa Sanata Biodun Olujimi ta karyata rade-radin cewa ta sanya daya daga cikin hadiminta ya mari wani ma’aikacin majalisar tarayya, inda shi kuma ya rama a kanta.

A jiya Litinin, 29 ga watan Janairu ne labarin marin da ake zargi Sanatan da sanyawa ayi cikin na’urar lift ya karade kafofin watsa labarai.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa sanatar ta maida martanin cewa ba ta sa a yi mari ba, kuma ba a mare ta ba,

“Ina sanar da jama’a cewa na halarciwajen taro, harma na shiga, sai kuma na tuna akwai wani taro a hawa na sama. Sai na shiga na’urar daukar jama’a. To a ciki akwai har da jami’in tsaro na, wanda ke kakkare mutane daga matsowa kusa da ni.

“A hakan ne kuma wani ya shigo ya na ta surfa zagin cewa ana kare waccan.” Haka sanatar ta shaida wa wasu ‘yan jarida.

KU KARANTA KUMA: Magu na so shugabannin Afrika su goyama yaki da rashawar Buhari baya

“Daga nan kuma wasu har da mace suka shigo su na ture shi, su na cewa shi wa ne, ya fita mana. Ni kuma sai na fito na ce abin da ake yi ba daidai ba ne."

Ta kara da cewa ta yaya za ta sa a mari wani. An fito da shi, sannan kuma ta umurce shi da ya tafi, tunda dai ya san bai yi daidai ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng