Kannywood: Wata matashiya tayi balaguro daga jamhuriyyar Nijar zuwa Kaduna domin ganin Umar M. Shareef
Soyayya gamuwar jini, inji masu hikimar zance, hakan c eta faru a lokacin da wata matashiya mai suna Maryam yar shekara 17 tayi tattaki tun daga kasar nijar zuwa Najeriya kawai saboda ta hada ido da shahararren mawakin nan Umar M. Shareef.
Matashiyar ta fito ne daga yankin Maradi, inda ta bayyana cewa iyayenta basa tare da juna sannan kuma ita ta kasance mai yawan awo hakan ya sa mahaifiyarta ke zarginta da aikata masha’a.
A cewarta wannan zargi ne ya fusata ta har ta yanke shawarar zuwa Kaduna don ta hadu da gwaninta Umar suyi waka babu mamaki hakan zai sa ta samu sukuni a zuciyarta.
KU KARANTA KUMA: Masu garkuwa da mutane sun saki yaron dan majalisa a Zamfara
Kamar yadda wani majiyi Umar Ridwan ya sanar, kimanin kwana biyu kenan tayi a Kaduna inda take neman gwarzonta ruwa a jallo.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng