An kunyata Gwamna bayan masu sauya sheka daga PDP 4000 sun ki bayyana
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya koma gida cike da jin kunya lokacin da masu sauya sheka 4000 daga jam’iyyar PDP suka ci bayyana a wani gangami kamar yadda aka sanar da farko.
Badaru ya kasance a karamar hukumar Birnin Kudu dake jihar a ranar Lahadi, wajen tarban masu sauya sheka da kuma kaddamar da ayyuka.
Magaji Da’u Aliyu, dan majalisar dake wakiltan mazabar Birnin Kudu/Buji a majalisar tarayya ne ya shirya taron, an kuma shirya taron ne domin bayar da tallafin ababen hawa ga amintattun jam’iyyar da kuma bayar da tallafin naira miliyan 2 ga daliban akarantun jami’aq wadanda suka fito daga mazabar.
Danmalam Unguwarya, shugaban masu sauya shekar ya gasa bayyana a lokacin da aka kira shi domin ya gabatar da jawabi a madadin masu sauya shekarhaka zalika babu wani wakilinsa ko masu sauya shekar da suka bayyana a wajen.
KU KARANTA KUMA: Kisan miji: Za a fara sauraron shari’an Maryam Sanda a yau
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Badaru ya so ya ji kunya a wani taron siyasa bayan da matasa a wajen suka rika yi masa ihu a yayin da yaje karbar wasu 'yan jam'iyyar adawa na PDP ya zuwa APC a jihar a karamar hukumar Birnin Kudu.
Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, dakin taron ya harmutse ne yayin da Gwamnan ya anshi abun magana zai soma bayanin sa sakamakon ihu da matasa suka rika yi masa wanda yayi sanadiyyar dakatar da jawabin na sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng