Ba zan matsa wa matan Saudiyya sanya bakar abaya ba a nan gaba – Yarima mai jiran gado

Ba zan matsa wa matan Saudiyya sanya bakar abaya ba a nan gaba – Yarima mai jiran gado

Yarima Muhammad bin Salaman mai jiran gado a masarautar kasar Saudiya ya jadadda cewa ba zai tilastawa matan kasar ci gaba da sanya bakin abaya ba wanda ya kasance tufafi da suka saba ambafi da shi ba a nan gaba.

Ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a tashar talbijin din Amurka wato CBS.

Yayi wannan kalami ne jim kadan kafin ya gana da shugaba Donald Trump na kasar Amurka.

Ba zan matsa wa matan Saudiyya sanya bakar abaya ba a nan gaba – Yarima mai jiran gado
Ba zan matsa wa matan Saudiyya sanya bakar abaya ba a nan gaba – Yarima mai jiran gado

Ya kuma sanar da cewa zai juya wa akidar wahabiyanci baya don rungumar Islamar sassaucin ra'ayi,ya bai wa matan Saudiyya 'yancin tuka ababen hawa,halartar wasannin motsa jiki da zuwa gidajen kallo na sinima.

KU KARANTA KUMA: Kada ka sake takara – APP ga Buhari

A shekarar bana a karo na farko kenan a tsawon tarihin masarautar Saudiyya, aka gudanar da gasar gudun famfalaki na mata,haka zalika kasar ta bai wa wata mawakiya damar kyashewa a birnin Riyadh.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Yariman yace mutuwa ce kadai zata iya hana ci mulkin kasar Saudiyya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng