Mun cika alkawarinmu kan gyaran hanya – Buhari

Mun cika alkawarinmu kan gyaran hanya – Buhari

A ranar Litinin, 19 ga watan Maris Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da cewa gwamnati mai mulki ta cika alkawarin da ta dauka game da gyaran hanya.

Buhari ya kuma bayyana cewa gwamnatin zata ci gaba da aiki a kan hanyoyin kasar inda ya kara da cewa gwamnatinsa ta habbaka ayyukan kasar daga kaso 15% zuwa kaso 30%.

Ya bayyana hakan ne a Abuja a wajen wani taron wayar da kai kan ci gaban da aka samu a fannin hanyoyi.

Ma’aikatar ayyuka da gidaje ne suka shirya wannan taron.

Mun cika alkawarinmu kan gyaran hanya – Buhari
Mun cika alkawarinmu kan gyaran hanya – Buhari

Shugaban kasar wanda babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya karanto jawabinsa ya fada ma tawagar a wajen taron cewa gwamnatin tarayya na zuba hannun jari a fannin jirgin kasa domin rage matsin dake manyan tituna.

KU KARANTA KUMA: Dino Melanye: Za a shiga sabon yaki tsakanin INEC da Majalisar Najeriya

Buhari ya bukaci wadanda ke lamarin dasu samar da makoma da zai inganta tsarin hanyoyin kasar.

A halin yanzu, babban ‘Dan jaridan nan kuma mai gidan Jaridar Sahara Reporters Yele Sowore ya dage cewa zai fito takarar Shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa inda yace zai ba Shugaba Muhammadu Buhari kashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel