Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Majalisar jihar Kano ta dakatar da Ciyaman na karamar hukumar Danbatta, Alhaji Idris Haruna Zago, har na tsawon watanni shida. Majalisar ta dakatar da Zago sakamakon bayyana sirrin gwamnatin da kuma kin rantsar da kansiloli.
Wata Lauya mazauniyar jihar Legas, Udeme Odibi, wadda aka ruwaito cewa ta dabawa mijinta wuka, Otike Odibi, har lahira, ta amsa laifinta na kisan kai. ‘Yan Sanda sunce matar mai shekaru 47 ta kira mahaifiyarta a waya bayan kisan.
Jam’iyyar The Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kaduna ta tarbi mutane akalla 5,558 da suka sauya sheka daga jam’iyyar Progressives Congress a kananan hukumomi 23 dake jihar a ranar Litinin, 7 ga watan Mayu.
Tsohon gwamnan jihar Borno, kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta kasa, Sanata Ali Modu Sheriff ya samu gagarumar tarbar kusoshi da magoya bayan jam’iyyar APC, a birnin Maidugurin jihar Borno, biyo bayan ayyana aniyar sauya sheka.
Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumuni Kabir Usman, a ranar Litinin, ya bayyanawa shugaba Muhammadu Buhari cewa kisan da akeyi a fadin kasar nan da kuma barazana ga tsaro a kasar nan anayinshi ne don a kunyatar da gwamnatinsa
Shugaban kungiyar Yarabawa ta Oodua People’s Congress (OPC), Dr. Fredrick Fasehun yayi gargadi game da tsare Sanata Dino Melaye. Ya kuma nuna rashin jin dadinsa game da yanda hukumar ‘Yan Sandan Najeriya ke tsare dashi a asibiti.
A lokutan baya tsofaffi ne ake alakanwa da farin gashi a kai, wato Furfura, amma a zamanin da muke ciki abin ya sauya, sai kaga hata jariri ma ana haifansa da farin gashi a kai. Hakan ne ya sa wasu masana suka gudanar da bincike.
Sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani yace akwai bukatar kafa sabuwar jam’iyyar siyasa, wanda zai hada da mutane masu hankali, masu aikin yi da kuma matasa, wanda zai kai Najeriya ko ina ba.
Shugabannin kungiyar matasan Arewa sun bayyana cewa zasu gudanar da zaben ba’a ga dukkanin yan takaran shugaban kasa daga Arewa ciki harda shugaba Muhammadu Buhari, Atiku, Kwankwaso, Dankwabo, Tambuwal da Sule Lamido.
Aisha Musa
Samu kari