Kisan da akeyi don a kunyatar da gwamnatinka ne – Sarkin Katsina ga Buhari

Kisan da akeyi don a kunyatar da gwamnatinka ne – Sarkin Katsina ga Buhari

- Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumuni Kabir Usman, a ranar Litinin, ya bayyanawa shugaba Buhari cewa kisan da akeyi a fadin kasar nan da kuma barazana ga tsaro a kasar nan anayinshi ne don a kunyatar da gwamnatinsa

- Sarkin a jawabinsa yace maganin wannan matsala dake damun kasar nan shine addu’a, saboda haka yayi kira ga ‘yan Najeriya da masu son siyasa dasu dage da addu’a

- Shugaba Buhari ya fadawa Sarki cewa yazo fada ne don yayi masa ta’aziyyar rasuwar babban limamin masallacin sarkin Katsina, Alhaji Mohammadu Lawal

Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumuni Kabir Usman, a ranar Litinin, ya bayyanawa shugaba Buhari cewa kisan da akeyi a fadin kasar nan da kuma barazana ga tsaro a kasar nan anayinshi ne don a kunyatar da gwamnatinsa.

Sarkin a jawabinsa yace maganin wannan matsala dake damun kasar nan shine addu’a, saboda haka yayi kira ga ‘yan Najeriya da masu son siyasa dasu dage da addu’a, don samun saukin wadannan matsaloli dake fuskantar kasar nan.

Shugaba Buhari ya fadawa Sarki cewa yazo fada ne don yayi masa ta’aziyyar rasuwar babban limamin masallacin sarkin Katsina, Alhaji Mohammadu Lawal, wanda kamar aboki yake kuma mai mutum mai son addini.

Kisan da akeyi don a kunyatar da gwamnatinka ne – Sarkin Katsina ga Buhari
Kisan da akeyi don a kunyatar da gwamnatinka ne – Sarkin Katsina ga Buhari

Ya tabbatarwa Sarki cewa gwamnatinsa bazata huta ba har sai ta cika alkawurran data daukarwa ‘yan Najeriya da kuma magance rashin tsaro dake damun kasar.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya ziyarci fadar Sarkin Katsina don yin ta’aziyyar rasuwar babban Limamin masallacin jihar

Bayan haka gwamnatin jihar Katsina itama ta shiga cikin jimamin rashin babban Limamin masallacin Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Lawal, ta hanyar jawabin data fitar ta hannun babban mai bawa gwamna shawara ta fannin sadarwa, Abdu Labaran, inda gwamnan ya bayyana cewa rasuwar malamin babban rashi ne ga jihar ta Katsina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng