Sultan yayi magana akan zagin da El-Rufai yayima Sanatocin Kaduna

Sultan yayi magana akan zagin da El-Rufai yayima Sanatocin Kaduna

A ranar Talata, 8 ga watan Mayu Sultan na Sokoto, Sa’ad Abubakar ya gargadi gwamna Nasir El-Rufai da dukkan yan siyasan Kaduna da su dakatar da yada kalaman kiyayya a yayinda kasar ke shirin zabe 2019.

Ku tuna a ranar 29 ga watan Maris El-Rufai ya raba jihad a sanatoci uku na jiharsa kan sun ki amincewa da rancen da yayi niyan nema daga bankin duniya, inda hakan ya sa gwamnan ya zagi sanatocin uku, cewa su shegu ne marasa asali.

Don haka a yayinda yake gabatar da jawabinsa na kafin Ramadan wanda kungiyar Jama’atul Nasirul Islam, JNI ta shirya a Kaduna, Sultan ya bayyana cewa wannan dabi’a da gwamnan ke nunawa ya fara damunsa.

Saboda haka yayi kira ga yan siyasan Kaduna da su ajiye duk wata gaba sannan kuma su dainakalaman batanci saboda Kaduna ce war yankin.

KU KARANTA KUMA: Na zaci zaka gyarawa Trump zancansa cewa ba kiristoci kadai ake kashewa ba a Najeriya – Dan majalisa ga Buhari

Saboda haka yayi kira gayan siyasan Kaduna da su ajiye duk wata gaba sannan kuma su daina kalaman batanci saboda Kaduna ce war yankin.nbancen addinai, kabilanci da kuma al’ada.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel