Majalisar jihar Kano ta dakatar da wani shugaban karamar hukuma
- Majalisar jihar Kano ta dakatar da Ciyaman na karamar hukumar Danbatta, Alhaji Idris Haruna Zago, har na tsawon watanni shida
- Majalisar ta dakatar da Zago sakamakon bayyana sirrin gwamnatin da kuma kin rantsar da kansilolin da aka zaba da kuma sabawa yarjejeniyar da akayi a sakateriyar karamar hukumar
- Majalisar ta kuma umurci ciyaman din mai rukon kwarya da ya rantsar da kansilolin da aka zaba cikin awowi 24
Majalisar jihar Kano ta dakatar da Ciyaman na karamar hukumar Danbatta, Alhaji Idris Haruna Zago, har na tsawon watanni shida.
Majalisar ta dakatar da Zago sakamakon bayyana sirrin gwamnatin da kuma kin rantsar da kansilolin da aka zaba da kuma sabawa yarjejeniyar da akayi a sakateriyar karamar hukumar.
Majalisar ta kuma umurci ciyaman din mai rukon kwarya da ya rantsar da kansilolin da aka zaba cikin awowi 24.
Alhaji Ibrahim Ahmed Gama, daya daga cikin mambobin karamar hukumar Nasarawa, ya gabatar da lamarin ne a gaban majalisa saboda muhimmancinsa ga jama’a.
KU KARANTA KUMA: Lauya a jihar Legas ta siyo sababbin wukake don ta kashe mijinta – ‘Yan Sanda
A halin da ake ciki, dubban magoya bayan jam'iyyar APC a jihar Kaduna sun sauya sheka zuwa PDP.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng