Yaro ya bugi ubansa mai shekara 83 har lahira

Yaro ya bugi ubansa mai shekara 83 har lahira

Hukumar yan sandan jihar Enugu ta fara bincike akan lamarin yaron da aka zarga da kashe mahaifinsa a Ojinato, wani gari dake jihar.

Acewar jawabin, ba’a samar da ainahin sunan mai laifin na gaskiya ba amma ana cigaba da bincike.

An rahoto cewa dan marigayin Pa Nathaniel Chukwuemerie, 83, wanda ya fito daga Ogidi a karamar hukumar Idemili North ne ya kashe shi.

Jawabin ya yi bayanin cewa Chukwuemerie, ya hadu da ajalinsa ne bayan dansa mai suna ‘The Boy’ya rotsa masa kai da muciya kan lamarin da ba’a riga an bayyana ba.

An tattaro cewa bayan faruwar lamarin, an dauke shi zuwa asibiti inda anan ne wani likita ya tabbatar da mutuwar sa.

KU KARANTA KUMA: Harin Mubi: Atiku Abubakar ya kai tallafi

Gawar tasa na nan ajiye a wajen ajiye gawa na babban asibitin Oji River.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel