Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin Birnin Gwari
Jagoran Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da kazamin harin da wasu yan ta’adda suka kai kauyen Gwaska da ke karamar hukumar Birnin Gwari na Jihar Kaduna.
A harin kwanan nan, yan ta’addan sun hallaka akalla mutane 58, yayin da wasu kuma da dama suka jikkata.
A cikin jawabin da kakakin Guterres, mai suna Stephane Dujarric ta fitar, shugaban ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta kamo yan ta’addan sannan kuma ta hukunta su daidai abin da doka ta tanadar ga irin su.
Wasu rahotanni kuma sun tabbatar da cewa wadanda suka mutu sun kai mutum 70.
Shugaban ya kuma nuna damuwar sa ganin yadda ake ta samun tashe-tashen hankula a wannan shiyya.
KU KARANTA KUMA: An tsinci gawar wani dan kasar waje a wani Otal da ke Legas
Sai ya yi kira cewa Majalisar Dinkin Duniya za ta meni ta shiga a yi aiki tare domin a kawo karshen zubar da jinin da ake yawan yi.
Daga nan sai ya mika sakon ta’aziyyar sa ga iyakan mamatan gwamnatin Najeriya da kuma al’ummar ta baki daya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng