APC, PDP bazasu iya kai Najeriya inda take mafarkin zuwa ba – Shehu Sani

APC, PDP bazasu iya kai Najeriya inda take mafarkin zuwa ba – Shehu Sani

Sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani yace akwai bukatar kafa sabuwar jam’iyyar siyasa, wanda zai hada da mutane masu hankali, masu aikin yi da kuma matasa, wanda zai kai Najeriya inda take mafarkin zuwa.

A cewarsa, hakan ne kadai mafita ga kasar saboda babu daya daga cikin manyan jam’iyyun dake kasar da zasu iya hakan.

Sani,wanda ya kasance mamba na jam’iyyar All Progressives Congress, yace amincin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda akanta ne APC ta gina gwamnatin ta bai isa mulkar kasa kamar Najeriya ba.

Acewarsa amincin yayi kadan akan abun da ake bukata wajen tafiyar da kasa kamar Najeriya inda ya kara da cewa yaki da rtashawa bas hi kadai ne ginshiki ko shawarar day a kamata gwamnati ta fuskanta kawai ba.

APC, PDP bazasu iya kai Najeriya inda take mafarkin zuwa ba – Shehu Sani
APC, PDP bazasu iya kai Najeriya inda take mafarkin zuwa ba – Shehu Sani

Sani ya kara da cewa yayinda shugaba Buhari ya nuna aminci ta hanyar bayyana kadarorinsa na gaskiya mutane da dama dake gwamnatinsa sun gaza yin haka.

KU KARANTA KUMA: Matasa a Arewa na shirin gudanar da zaben sobin-tabi ga masu takara

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa wamnatin Shugaba Buhari ta kara tabbatar da kan ta wajen yaki da sata a Najeriya bayan da Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yayi wani jawabi kwanan nan.

Farfesa Yemi Osinbajo yace Gwamnatin su za ta cigaba da yin ram da Barayin Najeriya ana binciken su. Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana wannan ne lokacin da aka kaddamar da wani tsari na kananan ‘yan kasuwa a Garin Ondo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng