Harin Mubi: Atiku Abubakar ya kai tallafi

Harin Mubi: Atiku Abubakar ya kai tallafi

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai tallafi ga al’umman karamar hukumar Mubi da harin Boko Haram ya rutsa da su indaya bayar da gudunmawar naira miliyan 10.

Atiku ya danka wannan kudi ne a wata asusu na tallafi dake karkashin ikon asibitin gwamnatin tarayya dake Yola mai suna (Yola’s Paupers Funds’) domin tallafawawadanda ke kwance a asibitin.

Idan ba a manta ba a ranar Talatar makon jiya ne wasu yan kunar bakin wake da ake zaton ‘yan Boko Haram ne suka kai hari a masallaci da cikin kasuwar ‘yan gwanjo dake Mubi inda mutane 69 suka rasa rayukansu sannan da dama suka sami jikkata.

Harin Mubi: Atiku Abubakar ya kai tallafi
Harin Mubi: Atiku Abubakar ya kai tallafi
Asali: Depositphotos

"Zuciyata ta karaya matuka a lokacin da naga halin da wadannan mutane ke ciki a asibiti. Sannan ina Kira ga gwamnati da ta karkato akalar ta zuwa ga ganin tsaro ya wadata a kasar nan.” cewarsa.

KU KARANTA KUMA: Lauya a jihar Legas ta siyo sababbin wukake don ta kashe mijinta – ‘Yan Sanda

A karshe shugaban asibitin Auwal Abubakar ya mika godiyarsa a madadin marasa lafiyan ga tsohon mataimakin shugaban kasa sannan ya tabbatar masa cewa za su yi amfani da wadannan kudade yadda ya Kamata.

Idan bazaku manta ba Atiku Abubakar ya nuna ra’ayinsa na son takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa na 2019, inda ya sha alwashin gyara kasar cikin wani dan kankanin lokaci idan har aka zabe shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel