Matasa a Arewa na shirin gudanar da zaben sobin-tabi ga masu takara

Matasa a Arewa na shirin gudanar da zaben sobin-tabi ga masu takara

Shugabannin kungiyar matasan Arewa sun bayyana cewa zasu gudanar da zaben ba’a ga dukkanin yan takaran shugaban kasa daga Arewa ciki harda shugaba Muhammadu Buhari.

Sauran yan takaran da kungiyar ta lissafo sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na jihar Gombe, Tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmed Makarfi, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaaso, Gwamna Aminu

Da yake bada jawabin karbuwansa jim kadan bayan sake zabensa a matsayin shugaban kungiyar, Kwamrad Kabiru Yusuf yayi bayanin cewa za’a shirya zaben ne domin fid-da gwani da ra’ayinsa ya zo daidai da na matasan.

''Yan siyasa da dama ciki harda yan takara daga arewa sun nuna ra’ayinsu a zaben shugabancin kasa na 2019. Don haka zamu gudanar da zaben somin tabi domin fid-da gwani.

Matasa a Arewa na shirin gudanar da zaben sobin-tabi ga masu takara
Matasa a Arewa na shirin gudanar da zaben sobin-tabi ga masu takara

“Kwanan nan za’a gabatar da zaben a shafinmu na yanar gizo sannan kuma zai kwashi tsawon kwanaki 60 kafin mu sanar da sakamakon. Ina shawartanmu da muyi tunani da kyau kafin mu fid-da gwaninmu da kuma yanta shi.

KU KARANTA KUMA: Za mu cigaba da kama wadanda su ka saci kudin kasa - Osinbajo

“Babu wani gwaninta da zamu iya yi da yafi ba Najeriya irin shugabanci da ta cancanta a wannan karni. Dole a magance talauci da rashin tsaro dake arewa hakan kuma hakkinmu ne” Inji shi.

A halin dake ciki, Mun samu labari cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta kara tabbatar da kan ta wajen yaki da sata a Najeriya bayan da Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yayi wani jawabi kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel