Kada a kuskura Melaye ya mutu a tsare – Fasehun yayi gargadi
- Shugaban kungiyar Yarabawa ta Oodua People’s Congress (OPC), Dr. Fredrick Fasehun yayi gargadi game da tsare Sanata Dino Melaye
- Fasehun ya kuma nuna rashin jin dadinsa game da yanda hukumar ‘Yan Sandan Najeriya ke tsare dashi a asibiti
- Fasehun a jawabin da yayi a jiya, ya bayyana lamarin a matsayin keta hakkin dan adam daga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari
Shugaban kungiyar Yarabawa ta Oodua People’s Congress (OPC), Dr. Fredrick Fasehun yayi gargadi game da tsare Sanata Dino Melaye.
Fasehun ya kuma nuna rashin jin dadinsa game da yanda hukumar ‘Yan Sandan Najeriya ke tsare dashi a asibiti, musamman yanda suka kaishi asibitin a saman gado.
Fasehun a jawabin da yayi a jiya, ya bayyana lamarin a matsayin keta hakkin dan adam daga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.
Lokacin da yake kira da a gaggauta sakinsa, ya bukaci Sufeto janar na ‘Yan Sandan, Ibrahim Idris, da kuma jami’ansa dasu dauki matakin gaggauta sakinsa, saboda rashin yin hakan na shiga cikin tarihin shugaba Buhari na hakkin dan adam.
KU KARANTA KUMA: Duk wanda bai da katin zabe ba zai shiga coci na ba – Fasto ga masu bauta
Idan bazaku manta ba a makon da ya gabata ne yan sanda suka gurfanar da Sanata Dino a gaban wata kotun jihar Kogi inda aka kai shi kotun akan gadon marasa lafiya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng