Hanyoyin 5 da zaka dawwamar da soyayyarka a zuciyar matarka

Hanyoyin 5 da zaka dawwamar da soyayyarka a zuciyar matarka

Aure sunnah ce ta ma’aiki sannan kuma ya kasance buri ga dukkanin masoyya, saboda ta hakan ne zasu nuna gwanjinsu wajen farantawa juna.

Sai dai kash, aure a zamanin da muke ciki ya zama tamkar wasan yara musamman a wajen Malam Bahaushe saboda rashin martaba shi da ba a yi.

Sau tari za ka samu da an fara zaman soyayyar ta ke gushewa sabida ma’auratan sun gaza wajen kiyaye wasu ginshikan soyayya da ke karfafa kauna a zukatan juna.

Hanyoyin 5 da Zaka dawwamar da soyayyarka a Zuciyar matarka
Hanyoyin 5 da Zaka dawwamar da soyayyarka a Zuciyar matarka

Da zarar an fara samun matsaloli nan da can kuma sai ka ga duk an fara gundurar juna. Sai danganta ta yi tsami. Sai rashin kyautatawa ta biyo baya, daga nan kuma sai ka ji ko dai mijin ya furta saki, ko kuma matar ta nemi a saketa saboda zaman ya ki dadi.

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta cancanci canji, wani wa’adin na mulkin Buhari matsala ce - Adeniran

Wadannan hanyoyi guda 5 in aka rike su sau da kafa za su dawwamar da soyayyar mata a zuciyar mijinta.

1. Ka zamo mai tausasa zance a wajen matarka, kar ka zamo mafadaci.

2. Idan ka shiga gida ka shiga da sallama domin tana korar shedan daga gida.

3. Idan tazo zata zauna ka tashi ka bata wurin zamanka, hakan zai tausasa zuciyarta.

4. Idan zaka bata shawara ko zaka yi mata fada ya zamo a cikin sirri, wato alokacin da kuke ku kadai, kada ya zamo a cikin mutane dan yin hakan muzantawa ne.

5. Ka zama mai kyautatawa matarka, hakan yana qara soyayya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel