Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Fulani na Kungiyar Miyetti Allah

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Fulani na Kungiyar Miyetti Allah

  • An kashe shugaban kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN a jihar Benue, Ardo Muhammad, tare da wani mutum Yakubu Isah a Otukpo
  • An kai harin ne bayan shugaban MACBAN ya halarci taron zaman lafiya da aka shirya tsakanin al’umma da makiyaya a Ohinmini
  • Kisan ya jawo tashin hankali a yankunan Otukpo da Ohinmini, yayin da ‘yan sanda suka fara bincike don gano wadanda suka kai harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Benue - Wasu 'yan bindiga sun kai wa shugaban kungiyar Miyetti Allah ta (MACBAN) a jihar Benue, Ardo Muhammad hari a karamar hukumar Otukpo, inda suka kashe shi.

An kashe shi tare da wani mutum mai suna Yakubu Isah, lamarin da ya jawo tashin hankali a wasu sassan Otukpo da kuma karamar hukumar Ohinmini da ke makwabtaka da ita.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya kawo hanyar magance rikicin manoma da makiyaya

'Yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah a Benue
Wasu Fulani da suka rasa muhallansu suna kokarin hada bukkar da za su zauna a sansanin Faladie. Hoto: MICHELE CATTANI/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

An kai harin ne bayan taron sulhu

Rahoton Punch ya bayyana cewa shugaban MACBAN ya halarci wani taron zaman lafiya da ake zargin jami’in ‘yan sanda na Ohinmini ya shirya tsakanin shugabannin al’ummar Ayunne da makiyaya a ranar Juma’a.

An ce taron ya kasance wani yunkuri na sasanta rikicin da ya taba faruwa a yankin, inda aka samu asarar rayuka a baya.

Bayan kammala taron, Ardo Muhammad da abokin tafiyarsa suka dauki haramar komawa gida, tafiyar da ba su karasa gidan ba kenan.

An kashe shugaban Miyetti Allah

A yayin da suke kan hanya, rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun yi musu harin kwanton bauna a wani kauye da ke karamar hukumar Otukpo.

Daya daga cikin ‘ya’yan marigayin ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tare motar mahaifinsa kuma aka kashe shi.

Shugaban karamar hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce kisan ya haifar da fargaba da tashin hankali a yankin.

Kara karanta wannan

Babbar mota ta burma kan 'yan APC suna tafiya kamfen, an samu asarar rai

Ya ce:

“Gaskiya ne an kashe shugaban MACBAN na jihar a karamar hukumar Otukpo a yau. Wannan kisan ya jawo tashin hankali a yankin da kewaye.”

Sai dai ya bukaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa jami’an tsaro suna kan lamarin.

Shugaban karamar hukumar Ohinmini, Adole Gabriel, ya ce shugaban MACBAN ya mutu ne a hanyar komawa gida bayan ya halarci taron zaman lafiya da jami’in ‘yan sanda na yankin ya kira.

'Yan bindiga sun hallaka shugaban Fulani a hanyar dawowa daga zaman sasanci
Taswirar jihar Benue, inda 'yan bindiga suka kashe shugaban Miyetti Allah. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun fara bincike

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Benue, DSP Udeme Edet, ta tabbatar da samun rahoton lamarin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Rahoton ya ruwaito Udeme ta ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata harin tare da daukar matakin da ya dace.

Wasu garuruwa a Otukpo da Ohinmini sun dade suna fuskantar hare-haren da ake zargin wasu makiyaya dauke da makamai ne ke kaiwa.

Kara karanta wannan

NASFAT ta ja hankalin musulmai, ta nemi su taimaka kan matsalar tsaron Najeriya

An kashe shugaban Miyetti Allah a Filato

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah na Barkin Ladi, Muhammad Adamu, a gidansa bayan ya gama shan ruwa.

Kungiyar MACBAN ta bayyana cewa marigayin ya tsallake yunkurin kisa sau uku a baya, amma wannan karo 'yan bindigar suka kashe shi.

An bayyana kisan Muhammad Adamu a matsayin abin bakin ciki, kasancewar ya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com