Lauya a jihar Legas ta siyo sababbin wukake don ta kashe mijinta – ‘Yan Sanda

Lauya a jihar Legas ta siyo sababbin wukake don ta kashe mijinta – ‘Yan Sanda

- Wata Lauya mazauniyar jihar Legas, Udeme Odibi, wadda aka ruwaito cewa ta dabawa mijinta wuka, Otike Odibi, har lahira, ta amsa laifinta

- ‘Yan Sanda sunce matar mai shekaru 47 ta kira mahaifiyarta a waya bayan kashe mijin nata cikin gaggawa don ta fada mata

- Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Legas Edgal Imohimi, a ranar Litinin ya tabbatarwa manema labarai aukuwar lamarin, yace wadda ake zargin ta aikawa kuma aikawa kanwarta da sakon waya na whatsapp

Wata Lauya mazauniyar jihar Legas, Udeme Odibi, wadda aka ruwaito cewa ta dabawa mijinta wuka, Otike Odibi, har lahira, ta amsa laifinta na kisan kai.

‘Yan Sanda sunce matar mai shekaru 47 ta kira mahaifiyarta a waya bayan kashe mijin nata cikin gaggawa don ta fada mata ta’addancin data aikata.

Lauya a jihar Legas ta siyo sababbin wukake don ta kashe mijinta – ‘Yan Sanda
Lauya a jihar Legas ta siyo sababbin wukake don ta kashe mijinta – ‘Yan Sanda

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Legas Edgal Imohimi, a ranar Litinin ya tabbatarwa manema labarai aukuwar lamarin a helikwatarsu dake Ikeja, yace wadda ake zargin ta aikawa kuma aikawa kanwarta da sakon waya na whatsapp, jim kadan kafin ta kashe mijin nata.

Kwamishinan ya kara da cewa wadda ake zargin ta samo saitin wukake wadanda a ciki ne tayi amfani da daya ta kashe mijin nata mai shekaru 50.

KU KARANTA KUMA: Mambobin APC da dama sun sauya sheka zuwa PDP a Kaduna

Punch Metro ta ruwaito cewa Udeme ta dabawa mijin nata wuka ne a ranar Alhamis data gabata a gidansu dake Diamond Estate, Sangote, AJah dake jihar Legas. Ta cire masa al’auransa ta saka masa a hannu kafin ta dabawa kanta wukar a ciki, wanda tayi sa’a bata mutu ba bayan ceto ranta da akayi a asibiti.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel