Mambobin APC da dama sun sauya sheka zuwa PDP a Kaduna
Jam’iyyar The Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kaduna ta tarbi mutane akalla 5,558 da suka sauya sheka daga jam’iyyar Progressives Congress a kananan hukumomi 23 dake jihar a ranar Litinin.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ta ruwaito cewa taron tarban nasu wanda aka gudanar a Zonkwa, karamar hukumar Zangon Kataf ya zamu halartan manyan masu ruwa da tsaki daga jam’iyyar PDP.
Ahmed Makarfi, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya bayyana lamarin a matsayin nasara sannan kuma ya shawarci masu sauya shekan da su hada hannu domin jam’iyar ta cimma manufarta.
Makarfi tsohon gwamnan jihar Kaduna ya nuna cewa ya tabbata jam’iyyar zata dawo da artabarta da ta rasa nan bada jimawa ba.
Ya bukaci mutanen das u fito kwan su da kwarkwatansu a ranar 1 ga watan Mayu sannan su zabi dan takarar PDP a zaben kananan hukumomi, “Dole mu tabbatar dam un kare kuri’unmu sannan mu kasa mu tsare saboda magudi.”
KU KARANTA KUMA: Ali Modu Sheriff ya samu kyakkyawar tarba daga APC a jihar Borno
A baya Legit.ng ta rahoto cewa , tsohon gwamnan jihar Borno, kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta kasa, Sanata Ali Modu Sheriff ya samu gagarumar tarbar kusoshi da magoya bayan jam’iyyar APC, a birnin Maidugurin jihar Borno, biyo bayan ayyana aniyar sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng