Ali Modu Sheriff ya samu kyakkyawar tarba daga APC a jihar Borno
Tsohon gwamnan jihar Borno, kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta kasa, Sanata Ali Modu Sheriff ya samu gagarumar tarbar kusoshi da magoya bayan jam’iyyar APC, a birnin Maidugurin jihar Borno, biyo bayan ayyana aniyar sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
A cikin jawabin da Sanata Modu Sheriff ya gabatar, a taron masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC yayi magana kan hadin kai, lalubo hanyoyin samun dawamamen zaman lafiya da kuma bunkasa jihar.
Ya kuma bayyana cewa cewa ya yafe wa duk wanda ya yi masa wani laifi, kuma ya sa kafa ya take abinda ya wuce.
KU KARANTA KUMA: Kisan da akeyi don a kunyatar da gwamnatinka ne – Sarkin Katsina ga Buhari
A jawabin gwamnan jihar Borno Kashem Shettima, ga kusoshin jam’iyyar, wanda da fari ya bayyana matukar jin dadin sa dangane yadda Ali Modu Sheriff tare da sauran wadanda suke mara masa baya wajen sake dawowa APC, ya ce wannan abin mutuntawa ne.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kashin Shettima da Ali Modu Sheriff sun sha alwashin ajiye gabar dake tsakaninsu domin su zama tsintsiya madaurinki daya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng