2027: Ana Zargin Goyon Bayan Sheikh Pantami Ya Jefa Kamfanin Gombawa Motors a Matsala

2027: Ana Zargin Goyon Bayan Sheikh Pantami Ya Jefa Kamfanin Gombawa Motors a Matsala

  • Mahukunta sun umarci kamfanin sufuri na Gombawa Motors ya fice daga tashar mota ta Ibrahim Hassan Dankwambo Mega Park cikin sa’o’i 24
  • Matakin ya zo ne kwanaki biyu bayan kamfanin ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamnan PDP, Farfesa Isa Ali Pantami
  • Mahukuntan Mega Park sun ce korar ta samo asali ne daga zargin karya ƙa’idojin aiki da koke-koken masu sufuri, ba saboda siyasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe, Nigeria - Gwamnatin Gombe karkashin Gwamna Inuwa Yahaya ta umarci kamfanin sufurin Gombawa Motors da ya tattara kayansa ya bar tashar motoci ta Ibrahim Hassan Dankwambo Mega Park cikin wa'adin awanni 24.

Matakin na zuwa ne kasa da kwanaki biyu bayan kamfanin ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a zaben 2027, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.

Kara karanta wannan

Tallar kosai da karago: 'Yan Najeriya sun dura kan matar Tinubu bayan kalamanta

Gombawa.
Motar sufuri ta kamfanin Gombawa Motors da ke jihar Gombe Hoto: Aliyu Usman
Source: Facebook

An ba kamfanin wa’adin sa’o’i 24

A cewar rahoton da Aminiya ta wallafa, umarnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 25 ga Yunin 2026, wacce shugaban kamfanin Principal Facilities Management Limited ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta bukaci Gombawa Motors da ya kwashe dukkan kayayyakinsa tare da barin harabar tashar motar ta Mega Park cikin sa'o'i 24.

Matakin ya jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke alakanta korar kamfanin da siyasa, musamman ganin cewa ya biyo bayan bayyana goyon bayan Gombawa Motors ga Pantami.

Kamfanin Principal Facilities Management Limited, wanda ke kula da gudanar da ayyukan tashar Ibrahim Hassan Dankwambo Mega Park a madadin Gwamnatin Jihar Gombe, shi ne ya fitar da umarnin.

Dalilin korar kamfanin Gombawa motors

A cewar sanarwar, mahukuntan tashar sun yanke hukuncin ne bisa zargin kamfanin da karya ƙa’idojin gudanar da ayyuka a bayan samun koke-koke daga sauran masu harkar sufuri.

Kara karanta wannan

Minista ya rutsa shugaban jami'a kan zargin nada hadimai 24 a ofishinsa

An kuma aika kwafin umarnin zuwa Kamfanin Kula da Hanyoyi da Sauran Ababen More Rayuwa na Jihar Gombe (GROCOL), Rundunar ’Yan Sanda, Hukumar DSS da Hukumar NSCDC.

Sai dai takardar ba ta ambaci cewa goyon bayan da kamfanin ya nuna wa Pantami ne ya jawo daukar wannan mataki a kansa ba.

Mahukuntan Mega Park sun nace cewa an ɗauki matakin ne saboda zargin karya dokokin aiki da kuma koke-koken masu ruwa da tsaki, ba saboda ra’ayin siyasa ba.

Kamfanin Gombawa Motors ya yi magana

A nasa ɓangaren, shugaban Gombawa Motors, Alhaji Ibrahim Mustapha, ya ce ƙungiyar ta amince da mara wa Farfesa Isa Ali Pantami baya, yana mai cewa sama da mambobi 4,000 ne suka goyi bayan wannan matsaya.

A rahoton Leadership, Mustapha ya kuma bayyana cewa tun bayan fara amfani da Mega Park, an sha sauya wa kamfanin wuraren aiki, lamarin da ya jawo musu babbar asarar kuɗi.

Pantami.
Dan takarar gwamnan jihar Gombe na jam'iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Ya ce sun kashe fiye da Naira miliyan 10 wajen gina tantuna, ofisoshi da sauran kayayyakin aiki a wani wuri da aka ware masu kafin daga bisani aka sake umartar su su koma wani wuri.

Kara karanta wannan

'Ya yi kadan': Gwamnatin Tinubu za ta sake duba mafi ƙarancin albashin N70, 000

Pantami ya karbi shaidar takara a PDP

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta mika wa Farfesa Isa Ali Pantami takardar shaidar zama ɗan takarar gwamnan Gombe a zaben 2027.

Pantami ya karbi takardar shaidar ne ranar a taron Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na jam’iyyar a hedkwatar PDP da ke birnin Abuja.

Bayanai sun nuna cewa shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP daga sassan kasar nan daban-daban sun halarci taron NEC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262