Aisha Khalid
4688 articles published since 22 Agu 2019
4688 articles published since 22 Agu 2019
Jimillar mutane takwas sun rasa rayukansu a karshen makon nan yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki wani gidan giya da matsayar sojin Najeriya a jihar Anambra.
Dakarun jami'an tsaron hadin guiwa na kasashe (MNJTF) sun sheke 'yan Boko Haram 22 ko 'yan ta'addan ISWAP yayin da suke cin karensu ba babbaka a tafkin Chadi.
Ghasoon Najimi, wata malamar makaranta wacce ke kan hanyarta ta zuwa makaranta dauke da kyautuka da niyyar raba musu ta tafka hatsari ta rasa ranta a Saudi.
Ana dab da buda baki, wani mutumi ya garkame mahaifinsa, mahaifiyarsa, 'dansa da 'diyarsa, wadanda ke azumi a gidan a Saudiyya gami da banka wa gidan wuta.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano(PCACC) da aka dakatar, Muhuyi Rimingado ya samu 'yanci bayan cika ka'idojin da aka gindaya masa.
An yi jana'iza tare da birne gawar wannan fitaccen biloniyan kuma mamallakin Otel din Tahir Guest Palace, 'dan kasar Lebanon, Tahir Fadlallah, a birnin Kano.
Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana kafa Kungiyar Kare Hakkokin Fulani Makiyaya mai suna NORIC. Ya bukaci makiyaya da su miko kokensu ga kungiyar, za ta bi musu hakki.
A ranar Alhamis wani mutumi 'dan shekara 40 mai suna Muazu Garba,ya rasa rayuwarsa yayin da ya yi kokarin ciro wayarsa, wacce ta fada masai a Jirgiya Quarters.
Wasu 'yan gwagwarmayar kasa Pakistan sun shiga hannu, an yanke musu hukuncin shekaru 5 a gidan yari, cin su tarar SR60,000, tare da haramta musu Hajji da Umra.
Aisha Khalid
Samu kari