Kano: An sako Muhuyi Rimin Gado daga gidan yari bayan cika sharuddan beli

Kano: An sako Muhuyi Rimin Gado daga gidan yari bayan cika sharuddan beli

  • An bada belin tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa a jihar Kano, Muhuyi Rimingado, bayan ya cika sharuddan da aka gindaya masa na belinsa
  • An tattaro yadda wata kotun majistare karkashin jagorancin babban alkali Aminu Gabari ta bada belinsa a ranar Juma'a bayan kama shi da aka yi a ranar Alhamis
  • Sai dai ya musanta lafin da kotu ke tuhumarsa na bayar da bayanin bogi, wanda yaci karo da sashi na 149, a kundin shari'ar na shekarar 2019

Kano - Tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa na jihar Kano (PCACC) da aka dakatar, Muhuyi Rimingado ya samu 'yanci bayan cika ka'idojin da aka gindaya masa kafin a sake shi.

Daily Nigerian ta tattaro yadda Rimingado ya sake ganawa da iyalinsa a gidansa dake titin Yahaya Gusau.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Kano: An sako Muhuyi Rimin Gado daga gidan yari bayan cika sharuddan beli
Kano: An sako Muhuyi Rimin Gado daga gidan yari bayan cika sharuddan beli. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Wata kotun majistare dake Kano karkashin jagorancin babban alkali Aminu Gabari ta bada belin Rimingado a ranar Juma'a bayan gurfanar dashi da aka fara yi.

A ranar Alhamis, 'yan sanda sun damko tsohon shugaban PCACC a masaukin bakin gwamnan jihar Sakkwoto a Abuja, inda yaje a tantance shi a matsayin 'dan takarar gwamna a Jam'iyyar PDP.

An gano yadda 'yan sandan suka yi awon gaba da shi ba tare da jinkiri ba bayan an tantance shi, gami da mika shi Ofishin rundunar dake FCT, daga bisani suka maido shi Kano don ya fuskanci laifin da ake tuhumarsa da shi.

Ana tuhumar Rimingado da bada bayanin bogi, wanda yaci karo da sashi na 149, na kundin tsarin shari'ar laifuka na 2019.

Ya musanta laifi dayan da ake tuhumarsa da shi

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Ko bayan gurfanar da Rimin Gado a gaban kotun, ya musanta aikata abinda ake zarginsa da shi.

Yayin sauraran shigar da bukatar belin, Gabari ya bada belin Rimingado akan N500,000 tare da tsayayyu guda biyu, wadanda dole su kasance kawunsa na wurin uba ko na wurin uwa, sannan ya gabatarwa kotu da shaidar biyan kudin haraji na shekaru uku.

Har ila yau, kotun ta umarci wanda ake karewa da ya gabatar da babban limamin masallacin Sharada, ko shugaban yankin Sharada a cikin wadanda za su yi belinsa.

Haka zalika kotun ta umarci Rimingado da ya aje wa kotu fasfotinsa na fita kasar waje don a mika shi ga babban magatakarda jihar Kano.

An damke tsohon shugaban hukumar rashawa a Kano, Muhyi Rimin Gado

A wani labari na daban, jami'an hukumar yan sanda sun damke tsohon shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da rashawa a jihar Kano PCACC, Muhuyi Magaji Rimin Gado.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Daily Nigerian ta ruwaito cewa an damke Rimin Gado ne a masaukin gwamnan jihar Sokoto dake birnin tarayya Abuja.

An tattaro cewa ya je gidan masaukin ne halartan zaman tantance yan takaran gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel