Anambra: Rayuka 8 sun salwanta bayan 'yan bindiga sun kai hari gidan giya da madakatar sojoji

Anambra: Rayuka 8 sun salwanta bayan 'yan bindiga sun kai hari gidan giya da madakatar sojoji

  • 'Yan bindiga sun halaka a kalla mutane takwas a karshen mako bayan sun auka wani gidan giya da madakatar sojoji a jihar Anambra
  • An gano yadda wasu hatsabiban da ba a san ko su waye ba suka fada gidan giya, gami da halaka wasu kwastomomi tare da mai wajen cin abinci
  • Haka zalika, sun halaka mutane uku a matsayar sojoji a Agulu dake karamar hukumar Anaocha bayan jami'an tsaron sun budewa hatsabiban wuta

Anambra - Jimillar mutane takwas sun rasa rayukansu a karshen makon nan yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki wani gidan giya da matsayar sojoji a jihar Anambra.

'Yan bindigan sun halaka mutane biyar a daren Juma'a a gidan giya a Osumenyi, cikin kudancin karamar hukumar Nnewi, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Anambra: Rayuka 8 sun salwanta bayan 'yan bindiga sun kai hari gidan giya da sansanin sojoji
Anambra: Rayuka 8 sun salwanta bayan 'yan bindiga sun kai hari gidan giya da sansanin sojoji. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Sauran mutane uku sun rasa rayukansu ne yayin da jami'an tsaro suka tasarwa 'yan bindigan da harbi a wata matsayar sojoji a Agulu, karamar hukumar Anaocha, kusa da gidan tsohuwar ministan labarai, marigayiya farfesa Dora Akunyili.

Ganau ya bayyana yadda aka tsinci gawawwakin mutane biyar a gidan giya bayan aukuwar lamarin, sai dai wata majiya ta ce wadanda lamarin ya ritsa dasu sun fi haka.

Vanguard ta ruwaito cewa, lamarin ya auku ne a wani wurin shakatawa cikin kauyen Obofia dake yankin da aka fi sni da Uto Ndu, wanda ya ritsa da mai wurin.

Yayin da aka tuntubi kakakin 'yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu, ya bayyanawa yadda rundunar bata samu wani rahoto mai kama da hakan ba.

Sai dai, ya ce rundunar na kokarin ganin ta tuntubi wajen da aka ce lamarin ya auku.

Kara karanta wannan

Hoton Kwamandan Sojin da yan bindiga suka sace a Taraba ya bayyana

Amma wani babban jami'in 'yan sanda a jihar wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya kara da cewa hakan ya auku ne misalin karfe 8:30 na daren Juma'a.

Majiyar ta kara da cewa, an turo da jami'an tsaron sojoji da 'yan sanda da sauransu yankin, kuma suna kokarin ganin lamarin bai sake maimaita kanshi ba.

Amma kuma, babu wanda ya san dalilin irin harin a anguwa mara hayaniya irin wannan.

A cewar majiyar, "'yan bindigan sun shiga wurin gami da budewa kwastomomi dake shaye-sheye cikin nishadi wuta, inda suka halaka mutane duk a gidan abincin."

'Yan bindiga sun kai wa motar kudi farmaki a Imo

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun bude wuta kan wata motar banki dake tafiya daga Mbaise zuwa Owerri a ranar Alhamis a karamar hukumar Mbaise da ke jihar Imo.

Vanguard ta tattaro cewa, lamarin ya faru wurin karfe 2 na rana a Ogbor Nguru dake Nwankwo a karamar hukumar Mbaise a jihar.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 6 Yayin Da Suka Kai Wa Tawagar Kwamanda Hari a Taraba

The Cable ta ruwaito cewa, an gano cewa, 'yan bindigan na kyautata tsammanin cewa motar dankare take da kudi kuma za ta kai su inda ya dace ne amma sai suka same ta babu komai ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng