Tsanantar harin 'yan bindiga: Hotunan mazauna kauyukan Zamfara suna kaura daga gidajensu

Tsanantar harin 'yan bindiga: Hotunan mazauna kauyukan Zamfara suna kaura daga gidajensu

  • Mazauna kauyen Magazu da wasu kauyukan kewaye na karamar hukumar Tsafe suna kaura domin barin gidajensu na gado
  • Jama'ar cike da tashin hankali sun sha alwashin kin komawa gida har sai tsaro ya inganta domin sun zargi gwamnati da nuna musu halin ko in kula
  • Mutanen da aka gani daddaure da kayansu, yaransu na biye da su a bakin titi tare da dabbobinsu, sun ce tun ranar Litinin ake kai musu hari

Tsafe, Zamfara - Mazauna kauyen Magazu da kewaye a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara sun fara barin gidajensu na gado sakamakon tsanantar farmakin 'yan bindiga da kuma garkuwa da mutane.

Wasu daga cikin mazauna yankunan an gansu tsaitaye a bakin titi da 'ya'yansu, kayansu a daddurae da dabbobinsu biye da su, TVC News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Kanam: Yadda gwamna Lalong ya yi watsi da gargadin da nayi masa – Shugaban karamar hukuma

Tsanantar harin 'yan bindiga: Hotunan mazauna kauyukan Zamfara suna gudun hijira
Tsanantar harin 'yan bindiga: Hotunan mazauna kauyukan Zamfara suna gudun hijira. Hoto daga @tvcnewsng
Asali: Twitter

Premium Times ta ruwaito cewa, sun sha alwashin ba za su sake komawa gidajensu ba har sai tsaro ya tabbata a yankin.

Yankin Magazu ya kasance madaddalar 'yan bindiga inda suka matsantawa domin kua tun ranar Litinin da ta gabata suka kai farmaki har zuwa yau babu sauki, lamarin da ke cigaba da kawo rashin rayuka da salwantar dukiyoyi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumomin 'yan sanda na jihar Zamfara a ranar Talata da ta gabata sun tabbatar da sace mutum ashirin da hudu da suka hada da mata da kananan yara, kuma har yanzu suna hannun miyagun.

Wannan lamarin na zuwa ne kasa da sa'o'i 12 bayan 'yan bindiga sun kai sabon farmaki kauyukan.

Mazauna kauyen sun koka kan yadda ba a samun jami'an tsaro suna kai musu dauki duk kuwa da yadda 'yan bindigan ke dadewa suna cin karensu babu babbaka.

Kara karanta wannan

Fusatattun Matasa sun fitittiki Sanata a mazabarta a Jos, sun kona motar yan jarida

Duk kokarin jn ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu ya gagara saboda baya daga kiran da ake masa.

Hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Leggi Jibrin, ya shiga hannun sojojin Najeriya

A wani labari na daban, fitaccen gagararren shugaban kungiyoyin ta'addancin da suka addabi yankunan jihohin Benue, Nasarawa da Taraba, Leggi Jibrin, ya shiga hannun jami'an tsaro bayan artabun musayar wuta da yayi da dakarun sojin rundunar Operation Whirl Stroke, rundunar tsaro ta hadin guiwa dake kula da jihohin uku.

Vanguard ta ruwaito cewa, an tattaro daga bakin majiyar tsaro, cewa dan bindigan da OPWS ta dade tana nema ya shiga hannun sojoji ne a kauyen Agam/Gidan Bawa dake karamar hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa yayin da suka fita aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel