Matsala na Neman Kunno Wa ga Atiku a cikin ADC kan Zaben 2027
- Wasu shugabannin ADC a Kudu-maso-Yamma, ciki har da ’yan takarar gwamna, sun yi zargi kan Atiku Abubakar
- Shugabannin sun kai ƙorafinsu ga Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Rauf Aregbesola, a wani taro da suka gudanar a Ibadan ranar 4 ga Satumba
- Mataimakin Atiku ya musanta zargin, yana mai cewa har yanzu ba a kafa ko ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓe na jihohin yankin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wasu manyan shugabannin ADC a yankin Kudu-maso-Yammacin Najeriya sun nuna rashin jin daɗinsu kan abin da suka bayyana a matsayin mayar da tsarin jam’iyyar saniyar ware da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ke yi gabanin zaɓen 2027.
Shugabannin, waɗanda suka haɗa da wasu shugabannin jam’iyyar na jihohi da ’yan takarar gwamna, sun zargi Atiku da gudanar da harkokinsa na siyasa a yankin ta hannun abokansa da na kusa da shi.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta tattaro cewa lamarin na haifar da rashin jituwa tsakanin mambobin jam’iyyar, tare da rage saurin gudanar da ayyukan yaƙin neman zaɓen Atiku a yankin.
An kai ƙorafi ga Aregbesola a Ibadan
Rahotanni sun nuna cewa ’yan takarar gwamna da wasu shugabannin ADC sun gudanar da wani taro a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ranar 4 ga Satumba.
A yayin taron, sun kai ƙorafinsu ga Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Ogbeni Rauf Aregbesola, inda suka nuna damuwarsu kan yadda Atiku ke gudanar da harkokinsa ba tare da haɗa tsarin jam’iyyar a yankin ba.
Shugabannin sun nemi sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa ta fayyace ko Atiku na da niyyar yin aiki tare da shugabannin jam’iyyar ko kuma ya fi son tafiyar da harkokinsa ta hannun abokansa da na kusa da shi.
Ɗaya daga cikin ’yan takarar gwamnan da suka halarci taron ya bayyana a ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoban 2026 cewa kusan dukkan shugabannin ADC a yankin sun nuna damuwa kan lamarin.
Sai dai ya yi magana ne bisa sharaɗin ɓoye sunansa saboda yadda batun yake da muhimmanci, inda ya ce ba a samu wani gagarumin sauyi ba tun bayan da suka gabatar da ƙorafinsu.
Atiku ya yi taro da shugabannin yankin
Wani shugaban ADC da ya halarci taron ya bayyana cewa bayan an gabatar da ƙorafin, an tilasta wa Atiku gudanar da taron intanet da shugabannin jam’iyyar na Kudu-maso-Yamma washegari, ranar 5 ga Satumba.
A cewarsa, Atiku ya tabbatar musu da cewa yana tare da jam’iyyar, tare da alƙawarin magance matsalolin da suka gabatar.
Ya kuma ce Atiku ya buƙaci kowace jiha da ta miƙa sunayen mambobin jam’iyya guda biyar domin naɗa su cikin kwamitin yaƙin neman zaɓensa.
Shugaban ADC ya kare Atiku
Sai dai shugaban ADC na Kudu-maso-Yamma, Akin Omole, ya wanke Atiku daga zargin, yana mai cewa ba zai yiwu tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi watsi da abokansa saboda harkokin jam’iyya ba.
Omole ya bayyana cewa ADC haɗakar ƙungiyoyin siyasa ce da ta ƙunshi abokan Atiku a sassa daban-daban na ƙasar.
Ya ce haɗin gwiwar waɗannan mutane na da muhimmanci wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027.
Mataimakin Atiku ya musanta zargin
Da yake mayar da martani kan zargin, Daraktan Yaɗa Labarai na Dabarun Kamfen ɗin Atiku, Phrank Shaibu, ya musanta cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya mayar da shugabannin jam’iyyar na jihohin Kudu-maso-Yamma saniyar ware.
Shaibu ya ce zargin ba shi da tushe, domin har yanzu ba a sanar da masu gudanar da kamfen a jihohin yankin ba, balle a ƙaddamar da kwamitocinsu.
"Zargin cewa an mayar da shugabannin jam’iyyar na jihohin Kudu-maso-Yamma saniyar ware ba gaskiya ba ne. Har yanzu ba a sanar da masu gudanar da kamfen na jihohi da kwamitocinsu ba, balle a ƙaddamar da su.
"Saboda haka, babu wani tsarin yaƙin neman zaɓe na jiha da aka kafa sannan aka ware wasu daga cikinsa.” In ji shi.

Source: Facebook
Dan Atiku na goyon bayan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Abba Abubakar, ɗan Atiku Abubakar, ya yi magana kan bambancin ra'ayi na siyasa tsakaninsu.
Abba ya ce zai tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a Adamawa, jihar mahaifinsa, a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng


