Borno: Sojin Najeriya sun bindige 'yan ISWAP 22, sun kwato makamai a tafkin Chadi

Borno: Sojin Najeriya sun bindige 'yan ISWAP 22, sun kwato makamai a tafkin Chadi

  • Rundunar jami'an tsaron hadin guiwar kasashe (MNJTF) ta sheke 'yan Boko Haram da mayaken ISWAP 22 a yayin aiwatar da wani aiki a tafkin Cadi
  • Bayan bata-kashi tsakanin jami'an tsaron da hatsabiban, an gano yadda aka samo bindigogi kirar AK-47 guda 12, bindigar jigida guda daya, da wasu abubuwa masu fashewa
  • Duk da irin yadda 'yan ta'addan Boko Haram suka rike wuta, hakan bai hana jami'an tsaron amfani da dabarbaru wajen ganin sun yi fito-na-fito da su ba

Borno - Dakarun jami'an tsaron hadin guiwa na kasashe (MNJTF) sun sheke 'yan Boko Haram 22 ko 'yan ta'addan ISWAP yayin da suke cin karensu ba babbaka a tafkin Chadi.

Babban kakakin rundunar MNJTF a N'Djamena na Chadi, Kamarudeen Adegoke ne ya tabbatar da hakan a wata takarda da ta fita ranar Lahadi, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Borno: Sojin Najeriya sun bindige 'yan ISWAP 22, sun kwato makamai a tafkin Chadi
Borno: Sojin Najeriya sun bindige 'yan ISWAP 22, sun kwato makamai a tafkin Chadi. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Adegoke, laftanal kanal, ya ce an sheke 'yan ta'adda a Tumbun Rabo cikin karamar hukumar Abadam a ranar 27 ga watan Afirilu.

Ya ce: "Bayan aiwatar da aikin da jami'an sojin sama na Operation Hadin Kai da MNJTF suka yi, bayanin ya bayyana yadda ake sheke a kalla 'yan Boko Haram 22, tare da gano bindigun kirar AK-47 guda 12, bindigar jigida mai tsawon 60mm da manyan abubuwa masu fashewa daban-daban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Har ila yau, an gano motoci biyar na bindigu tare da tarwatsa motar kaya da hatsabiban ke amfani da ita wajen aikata ayyukan ta'addanci.
"Haka zalika, dakarun sun gano wata motar yaki ta MRAP; wacce aka taba satowa daga rundunar sojin kasan Najeriya a baya," a cewarsa.

Adegoke ya cigaba da bayyana yadda dakarun suka cigaba da sintiri don hurawa hatsabiban wuta.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Malaman makarantun Poly sun bi sahu, ASUP ta sanar da shiga yajin aiki

Duk da irin yadda 'yan ta'addan Boko Haram suka rike wuta, dakarun sojin kasan ba su yi kasa a guiwa wajen jajircewa don ganin sun yi fito-na-fito da hatsabiban ba.

Borno: 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari ana tsaka da shagalin biki

A wani labari na daban, an rasa ran mutum daya inda wasu da dama suka jigata yayin da mayakan ta'addancin Boko Haram/ISWAP suka kai farmaki wurin wani shagalin aure a kauyen Kindila na karamar hukumar Askira Uba ta jihar Borno.

Kamar yadda wata majiya ta sanar, maharan sun bayyana a cikin manyan motoci biyu kuma suka tare hanyar fita yayin da suke ta harbe-harbe kan duk wanda suka samu, al'amarin da yasa mutane suka dinga gudu domin tseratar da rayukansu, Aminiya Daily Trust ta ruwaito.

"Daga bisani miyagun sun halaka wani dan banga mai suna Suleiman sa'in da suka tafi da shi. An ga gawar marigayin," wata majiya ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Sojoji 6 sun kwanta dama yayin da yan bindiga suka farmaki wani kauyen a Taraba

Asali: Legit.ng

Online view pixel