Hotuna: An yi jana'izar biloniya mazaunin Kano, mamallakin Tahir Guest Palace

Hotuna: An yi jana'izar biloniya mazaunin Kano, mamallakin Tahir Guest Palace

  • An yi jana'izar fitaccen biloniya mai Otel 'dan kasar Lebanon, dake zaune a Kano, wanda ya kwanta dama a ranar Juma'a
  • Yayin da babban Kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Harun Ibn Sina, ya jagoranci sallarrr gawar mamacin a fadar sarkin Kano a ranar Asabar
  • Haka zalika, an gano yadda mukaddashin gwamnan Kano, Nasir Yusuf Gawuna da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero suka halarci jana'izar.

Kano - An yi jana'iza tare da birne gawar wannan fitaccen biloniyan kuma mamallakin Otel din Tahir Guest Palace, 'dan kasar Lebanon, Tahir Fadlallah, wanda ya rasu ranar Juma'a a Kano.

Daily Trust ta ruwaito cewa, babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Harun Ibn Sina ne ya jagoranci jana'izar mamacin a fadar sarkin Kano a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP

Hotuna: An yi jana'izar biloniya mazaunin Kano, mamallakin Tahir Guest Palace
Hotuna: An yi jana'izar biloniya mazaunin Kano, mamallakin Tahir Guest Palace. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daga cikin wadanda suka samu halartar sallar gawar sun hada da mukaddashin gwamna na jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muna fatan Ubangiji zai gafarta masa kurakurensa, gami da masa rahama, albarkar watan Ramadanan da muke ciki.

Sannan ya ba wa masoyansa hakurin jure rashinsa.

Hotuna: An yi jana'izar biloniya mazaunin Kano, mamallakin Tahir Guest Palace
Hotuna: An yi jana'izar biloniya mazaunin Kano, mamallakin Tahir Guest Palace. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Hotuna: An yi jana'izar biloniya mazaunin Kano, mamallakin Tahir Guest Palace
Hotuna: An yi jana'izar biloniya mazaunin Kano, mamallakin Tahir Guest Palace. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Hotuna: An yi jana'izar biloniya mazaunin Kano, mamallakin Tahir Guest Palace
Hotuna: An yi jana'izar biloniya mazaunin Kano, mamallakin Tahir Guest Palace. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Innalillahi: Allah ya yiwa hamshakin attajiri a Kano, Tahir Fadlullah rasuwa

A wani labari na daban, hamshakin attajirin nan mai shahararren otal din Tahir Guest Palace da ke Kano, Tahir Fadlullah, ya rasu.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu ne ya tabbatar da rasuwar Fadlullah ta shafinsa na Instagram da safiyar yau Juma’a.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan APC sun dira filin Malam Aminu Kano

Ya bayyana rasuwar mamallakin otal din a matsayin abin razanarwa, kuma ya yi addu’ar Allah ya jikansa ya kuma ba iyalansa hakurin rashi.

An samu labarin cewa Mista Fadlullah, wanda ya rasu a kasarsa ta haihuwa, Lebanon, za a binne shi ne a birnin Kano ta Najeriya, inda ya rayu tsawon shekaru da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel