Ana Shirye Shiryen Zaben 2027, Atiku Ya Mika Babbar Bukata ga INEC

Ana Shirye Shiryen Zaben 2027, Atiku Ya Mika Babbar Bukata ga INEC

  • Atiku Abubakar ya soki INEC bayan amincewa da cewa jami'anta sun shigar da hotunan da AI ta samar da bayanan bogi cikin rajistar masu kada kuri'a
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci INEC ta bayyana sunayen jami'an da ake zargi, ta fitar da hujjoji tare da mika wadanda abin ya shafa ga hukumomin tsaro
  • Atiku ya ce zargin cewa hotunan AI sama da miliyan 20 na iya kasancewa cikin rajistar ya sa ya zama wajibi a gudanar da binciken fasaha mai zaman kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da amincewar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) cewa an shigar da hotunan da aka samar ta hanyar fasahar AI da bayanan bogi cikin rajistar masu kada kuri'a.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya fadi abubuwa 3 za su ba Tinubu nasara a zaben 2027

Atiku ya ce wannan lamari ya kawo cikas ga amincin hukumar da kuma yadda ‘yan Najeriya ke kallon sahihancin tsarin zabe a kasar.

Atiku ya soki hukumar INEC
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Daraktan Yada Labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Phrank Shaibu, ne ya fitar da sanarwar Atiku ranar Juma'a, 30 ga watan Oktoban 2026 a shafinsa na X.

Atiku ya zargi INEC da gazawa

Atiku ya bayyana cewa abin damuwa ne yadda hukumar da aka dora wa alhakin kare kuri'un ‘yan Najeriya ta amince cewa tsarin rajistar masu zabe ya samu matsala daga hannun jami'an da aka damka wa aikin gudanar da shi.

"INEC ta amince cewa akwai wasu hotunan da aka samar ta hanyar AI a cikin rajistar masu kada kuri'a, kuma jami'an rajista sun shigar da bayanan da ba su dace ba a sassan kasar.
"Hukumar da aka dora wa alhakin kare kuri'un ‘yan Najeriya ta amince cewa mutanen da aka damka wa aikin gudanar da tsarinta sun lalata amincin wannan tsarin. Wannan babbar gazawa ce ta shugabanci da matakan kare bayanai." In ji shi.

Kara karanta wannan

INEC ta yi magana kan cire sunan Gwarzo daga jerin 'yan takarar gwamnan Kano

Atiku ya soki bayanin shugaban INEC

Atiku ya kuma soki bayanin Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, da Daraktan Fasahar Sadarwa ta Zamani (ICT), Dakta Lawrence Bayode.

Ya ce jami'an hukumar sun bayyana cewa sun san abin da wasu ma'aikatansu suka aikata da kuma yadda aka samu kutse cikin rumbun bayanan masu zabe, amma ba su san dalilin da ya sa aka aikata hakan ba.

Atiku ya ce irin wannan bayani bai wadatar ba, yana mai tambayar yadda bayanan miliyoyin masu kada kuri'a za su kasance cikin tsarin tsaro da ya kasa kai matsayin na manhajojin sada zumunta.

"Farfesa Joash Amupitan, ta bakin Bayode Lawrence, ya ce INEC ta san abin da jami'anta suka aikata da yadda suka yi kutse cikin rajistar, amma tana ikirarin ba ta san dalilin da ya sa suka yi hakan ba.
"Wannan kaucewa amsa tambaya ce abin kunya, ba cikakken bayani ba. Ko WhatsApp, Facebook da asusun imel na kashin kai suna da alamun sun fi tsarin tsaron da daraktan ICT na INEC ya bayyana a gidan talabijin na kasa karfi." In ji shi.

Kara karanta wannan

Dogara ya kare Tinubu kan rashin tsaro, ya fadi lokacin da matsalar ta fara

Atiku ya kuma tambayi yadda bayanan miliyoyin masu kada kuri'a a Najeriya za su kasance cikin tsarin da ba shi da ingantaccen tsaro kamar yadda ya kamata.

Wace bukata Atiku ya mika ga INEC?

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci INEC ta gaggauta fitar da dukkan hujjojin da ke nuna yadda aka samu matsalar, tare da bayyana sunayen jami'an da ake zargi da hannu wajen shigar da bayanan bogin.

Ya kuma nemi hukumar ta yi bayanin dalilin da ya sa ba a dakatar da jami'an da ake zargi ba, ko kuma mika su ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike da gurfanar da wadanda aka samu da laifi.

"Idan INEC ta san yadda aka lalata rajistar masu kada kuri'a, to dole ne ta fitar da hujjoji, ta bayyana dukkan jami'an da ke da hannu, sannan ta yi bayanin dalilin da ya sa ba a dakatar da su ba ko gurfanar da su a gaban kotu." In ji shi.

Ya kara da cewa bai kamata Shugaban INEC, Farfesa Amupitan, ya amince da cewa an samu matsala a tsarin hukumar ba tare da bayyana wadanda suka aikata hakan ba, sannan ya sa ran ‘yan Najeriya za su amince da cewa ba a san dalilin faruwar lamarin ba.

Kara karanta wannan

'Gyaran da Peter Obi zai yi a bangaren da Tinubu ya nakasa a Najeriya'

Atiku ya zargi INEC
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

INEC ta magantu kan batun dage zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar ba ta da shirin sauya ranar zaɓen 2027.

Ya ce an riga an tsara ranar zaɓen, kuma shirye-shiryen gudanar da shi sun yi nisa, saboda haka ba za a sauya jadawalin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng