Kalaman Sarkin Waka: Mun yi dawafi a kanka, mun hada ka da Allah, Jarumai maza a Saudiyya

Kalaman Sarkin Waka: Mun yi dawafi a kanka, mun hada ka da Allah, Jarumai maza a Saudiyya

  • Batun rikicin cikin masana'antar Kannywood yana cigaba da kamari inda wasu jarumai maza da suka je Saudiyya suka ce sun yi dawafi kan batun Sarkin Waka
  • Daga cikin jaruman akwai malam Ibrahim Sharukhan, Suleiman Costume, Sani Candy da kuma Adebo wadanda suka ce sun bar Naziru da Allah kan kalamansa
  • Sun zargi Sarkin Wakan da yi musu cin mutunci, bacin suna da kazafi duk da su sana'arsu suke yi, sun ce sun bar shi da Allah kan kalamansa

Batun rigimar Sarkin Waka da Nafisa Abdullahi, duk da dai wadanda suka fara rigimar sun yi shiru, wasu daga cikin 'yan masana'antar shirya fim basu bar maganar ba.

Har yanzu a nan da chan ana dan jin maganganu da rubuce-rubuce na nuna rashin jin dadin abinda sarkin wakan ya yi ga 'yan uwansa 'yan fim yayin da magoya bayansa na nasu rubutun musamman a Facebook da tiktok.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan Shi'a da jamian tsaro sun yi arangama, soji sun harbi mutum 8 a Zaria

Kalaman Sarkin Waka: Mun yi dawafi a kanka, mun hada ka da Allah, Jarumai maza a Saudiyya
Kalaman Sarkin Waka: Mun yi dawafi a kanka, mun hada ka da Allah, Jarumai maza a Saudiyya. Hoto daga @malamibrahimsharukhan
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da mafi yawan 'yan kannywood da suka halarci Saudiyya suka ki tofa nasu albarkacin bakinsu suka mayar da hankali kan ibadunsu, Malam Ibrahim Sharukhan, Sani Candy, Suleiman Costume da mai haska dandali kuma jarumi Adebo, sun bayyana cewa sun yi dawafi kuma sun kai karar Naziru wurina Allah kan abinda yake musu.

Kamar yadda Malam Ibrahim Sharukhan yace: "Da kai nake, Allah yasa kana ganewa. Wallahi, wallahi, wallahi muna garin ma'aiki kuma mun yi dawafi mun hada ka da Allah, munbar ka da Allah."

Sauran wadanda suka tofa albarkacin bakinsu a kan lamarin a cikin bidiyon da Malam Ibrahim Sharukhan ya saki a shafinsa na Instagram, sun hada da jarum kuma mai haska dandali, Adebo, Sani Candy da Suleiman Costume.

Ga bidiyon:

Kara karanta wannan

Kaduna: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake, Sun Buƙaci Man Fetur Da Katin Waya a Matsayin Kuɗin Fansa

Mai neman suna: Idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, Nafisa ga Sarkin Waka

A wani labari na daban, jaruma Nafisa Abdullahi ta yi martani ga fitaccen mawaki, Naziru Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Wakar San Kano.

A jiya ne mawakin yayi wata wallafa wacce kai tsaye wadanda ke bibiyar shafin jaruma Nafisa Abdullahi za su gane cewa martani ne yayi ga wata wallafar da tayi.

Jarumar ta caccaki iyayen da ke haihuwa tare da kin daukar dawainiyar 'ya'yan kuma su sake su a kan titi suna almajiranci babu tarbiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel