"Ba Sabon Alkawari ba"; Gwamna Radda Fadi Abin da Yake Kamfen da Shi
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya bayyana abin da zai yi yakin neman zabe da shi a kananan hukumomi
- Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa ba zai yi wa jama'a sababbin alkawura ba domin neman su sake ba shi kuri'unsu a zaben 2027
- Gwamnan ya bayyana cewa zai nuna ayyukan da ya gudanar domin su zama abubuwan da zai yi yakin neman zabe da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa nasarorin da gwamnatinsa ta samu a faɗin jihar su ne ginshiƙin neman sabon wa’adi a zaɓen 2027.
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne yayin babban taron yaƙin neman zaɓen Tinubu/Dikko na 2027 a Ƙaramar Hukumar Bakori.

Source: Facebook
Hadimin Gwamna Radda kan harkokin kafafen yada labarai, Mustapha Samaila Ingawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamban 2026.
“Muna gabatar da ayyukanmu ne a kowace Ƙaramar Hukuma. Ayyukan da muka gudanar muke yaƙin neman zaɓe da su, ba alkawura ba.” In ji shi.
Taron, wanda aka gudanar a Bakori, ya gudana cikin yanayi na farin ciki da ɗumbin jama’a, inda dubban magoya bayan APC daga sassa daban-daban na ƙaramar hukumar suka fito domin sake tabbatar da goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Radda.
Gwamna Radda ya kai ziyara fada
Tun da farko Gwamna Radda, ya kai ziyarar girmamawa ga Makaman Katsina kuma Hakimin Bakori, Alhaji Garba Tukur Idris, da Jarman Katsina kuma Hakimin Tsiga, Alhaji Dikko Tukur Idris.
A cikin jawabin maraba, Shugaban Ƙaramar Hukumar Bakori, Hon. Abubakar Musa Barde, ya yaba da ƙudurin Gwamna Radda na inganta rayuwar al’ummar yankin.
Radda ya fadi nasarorin gwamnatinsa
A nasa jawabin, Gwamna Radda ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a Bakori, ciki har da gina hanyoyin cikin gari guda tara masu tsawon kilomita 6.6, gina da gyaran cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu, tallafin noma, bayar da guraben karatu, da gyare-gyaren hukumomin gargajiya da na addini.
Gwamnan ya kuma yaba da inganta tsaro a yankin, tare da neman ci gaba da goyon bayan al’umma ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
A nasa jawabin, Hakimin Bakori, Alhaji Garba Tukur Idris, ya nuna godiya ga Gwamna Radda bisa cika alƙawuran da ya ɗauka, musamman gina Hanyoyi a cikin gari, samar da kayan aikin noma, tallafin karatu da shirye-shiryen bunƙasa al’umma.
Ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnatin wajen inganta tsaro da samar da damammakin ci gaba ga al’ummar Bakori.

Source: Facebook
Batun kona motocin APC a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta yi karin haske kan rikicin da ya faru a garin Yankara da ke karamar hukumar Faskari.
Gwamnatin ta bayyana cewa lamarin ba shi da alaka da gangamin yakin neman zaben Gwamna Malam Dikko Umaru Radda.
Asali: Legit.ng

