Da duminsa: Sheikh Gumi ya kafa kungiyar kare hakkin Fulani Makiyaya

Da duminsa: Sheikh Gumi ya kafa kungiyar kare hakkin Fulani Makiyaya

  • Sannannen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana kafa Kungiyar Kare Hakkin Fulani Makiyaya
  • Ya bayyana hakan ne a yayin wa'azi a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna inda yace kungiyar za ta saurari koken makiyayan tare da bi musu hakkinsu
  • Gumi ya sanar da cewa sabuwar kungiyar mai suna NORIC za ta samu shugabancin Farfesa Umar Labbo kuma tana kira ga makiyayan da su kai kokensu

Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Ahmad Gumi, ya sanar da cewa ya kafa kungiyar assasa kare hakkin Fulani makiyaya.

Gumi ya bada sanarwan kafa kungiyar wacce za a kira ta da Nomadic Rights Concern (NORIC) a yayin tafsirin watan Ramadan a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

Ya ce kungiyar za ta tattaro tare da bayyana irin cin zarafi da take hakkokin Fulani makiyaya da ake yi, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Group Admin ya yi 'batan dabo da N1.8m da mambobi suka hada a WhatsApp

Da duminsa: Sheikh Gumi ya kafa kungiyar kare hakkin Fulani Makiyaya
Da duminsa: Sheikh Gumi ya kafa kungiyar kare hakkin Fulani Makiyaya. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC
"Mun ga dacewar kafa Kungiyar Kula da Hakkokin Makiyaya, NORIC, wacce za ta samu shugabancin Farfesa Umar Labbo. NORIC za ta zama wata hanya da makiyaya za su mika korafinsu da damuwarsu zuwa ga hukumomin da suka dace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Da yawa daga cikinsu sun yi korafin cewa sun yi rashin 'yan uwansu. Wasu kuwa suna gidajen gyaran hali na tsawon shekaru ba tare da suna san laifukansu ba ko kuma na gurfanar da su.
“An kafa wannan kungiyar ne domin magance wadannan matsalolin kuma ana fatan makiyayan za su bi hanyar da ta dace wurin mika kokensu ba tare da tada hankula ba," Gumi yace.

Ya ce makiyayan za su iya mika korafe-korafensu ga NORIC, wanda zasu taimaka wurin daukan matakin shari'a don kwato musu hakkinsu.

Ku yi koyi da 'yan uwanku da suka tuba

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan Shi'a da jamian tsaro sun yi arangama, soji sun harbi mutum 8 a Zaria

Gumi ya yi amfani da wa'azin wurin kira ga 'yan bindiga da ke barna a kasar nan ballantana arewa maso yamma da su rungumi zaman lafiya tare da ajiye makamansu.

"Mun yi kira gareku da ku ji tsoron Allah tare da daukar hanyar zaman lafiya. Kuyi koyi da wasu daga cikinku da suka ajiye makamai, suka saki wadanda suka sace, suka tuba kuma suka nemi yafiyar Allah," Gumi yace.

A kan farmakin jirgin kasa na Kaduna, malamin ya yi kira ga 'yan bindigan da su sako wadanda suka sace tare da mika korafinsu kai waye.

Abinda Gumi ya sanarwa ‘yan bindiga da muka hadu da su a dajikan jihohin Arewa 8, Mamban NEF

A wani labari na daban, wani mamba a kungiyar dattawan Arewa, Usman Yusuf, ya bayyana abinda fitaccen malamin addinin Islama Ahmad Gumi, ya fada wa ‘yan bindiga da suka hadu da su a cikin dajikan jihohin Arewa takwas.

Kara karanta wannan

Tsanantar harin 'yan bindiga: Hotunan mazauna kauyukan Zamfara suna kaura daga gidajensu

A cewar dattijon, Gumi ya shaida wa ‘yan fashin wadanda yanzu aka ayyana a matsayin 'yan ta'adda, cewa kisa, fyade, raunata jama'a da kona dukiyoyin jama’a da na gwamnati ba abu ne da za a amince da su ba, kuma babu hujja kan abinda suke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel