Da duminsa: 'Yan Shi'a da jamian tsaro sun yi arangama, soji sun harbi mutum 8 a Zaria

Da duminsa: 'Yan Shi'a da jamian tsaro sun yi arangama, soji sun harbi mutum 8 a Zaria

  • 'Yan Shi'a da suka fito zanga-zanga sun yi karon batta da dakarun sojin Najeriya a karamar hukumar Sabon Garin Zaria
  • Al'amarin ya faru ne wurin karfe 2 na rana bayan saukowa daga sallar Juma'a inda 'yan Shi'an suka fito tare da toshe titi
  • Babu kakkautawa sojoji suka fara harbin kai mai uwa da wabi bayan isar su wurin, a take suka harbi 'yan shi'a 8

Zaria, Kaduna - Labari da duminsa da ke zuwa da yammacin nan shi ne na angamar Musulmi mabiya Shi'a da jami'an tsaro a garin Zaria.

'Yan shi'an sun fito tattaki da zanga-zanga inda bayanan da Legit.ng ta tattaro suka bayyana cewa sun fara tun daga Masallacin 'yan kaji da ke cikin kasuwar Sabon Gari a Zaria.

Kara karanta wannan

Tsanantar harin 'yan bindiga: Hotunan mazauna kauyukan Zamfara suna kaura daga gidajensu

Da duminsa: 'Yan Shi'a da jamian tsaro sun yi arangama, soji sun harbi mutum 8 a Zaria
Da duminsa: 'Yan Shi'a da jamian tsaro sun yi arangama, soji sun harbi mutum 8 a Zaria
Asali: Original

Ganau ba jiyau ba sun tabbatarwa da Legit.ng yadda 'yan Shi'an suka gangara a kasa suna tattakinsu tare da toshe hannu daya na tagwayen titin da ke PZ a Zaria.

Babu dadewa da hakan ne aka ga 'yan Shi'an sun fara kone-konen tayoyi a kan titin duk kuwa da cewa sun yi ikirarin zanga-zangar lumana suka fito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda wani mai siyar da wayoyi a rukunin shagunan PZ mai suna Imam Abu Rukayya, wanda aka fi sani da Young Professor, ya sanarwa Legit.ng:

"Al'amarin ya fara ne bayan saukowa sallar Juma'a. Mun ga 'yan sanda cike da mota biyu daga hedkwatar 'yan sandan Sabon Gari dake GRA ta fito kcikin hanzari tare da nufar hanyar kasuwa. Babu jimawa sai ga motocin sojoji bayan isowar 'yan shi'an, sun fara kona tayoyi a kan titi.

Kara karanta wannan

Hotuna: Sojin Najeriya sun ragargaji Boko Haram, sun halaka Amir da shugaban malaman 'yan ta'addan

"A take sojojin suka fara harbi inda jama'a da dama suka bar kayan sana'arsu tare da neman maboya. Ni kaina na nemi wurin buya.
"A daidai PZ wurin shagunan siyar da wayoyi, sojojin sun harbi 'yan Shi'a uku. Bayan sun gangara wurin bankuna kuma sun kara da harbar mutum biyar, wadanda daga baya muka ga ana daukesu da Napep."

Legit.ng ta ji ta bakin wani mai shagon siyar da wayoyi mai suna Sagir Mustapha wanda ya sake tabbatar da cewa bayyanar sojojin da kuma ganin suna harbin kan mai uwa da wabi ne yasa ya tsere gida domin gudun cutuwa.

Sai dai Malam Sanusi Lawal, mai sana'ar siyar da waya duk a PZ din Zarian, wanda komai ya faru a kan idonsa, ya tabbatarwa da Legit.ng cewa mutum takwas daga cikin 'yan shi'an sun jigata sakamakon harbin da sojojin suka yi musu.

Sai dai yace bashi da tabbacin idan wani daga ciki ya rasa ransa duk da ya tabbatar da jigatarsu kuma a kan idonsu lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An tsaurara matakan tsaro yayin da yan takara suka fara dira Sakatariyar PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel