Malama ta tafka hatsari, ta rasu tana hanyar kai wa dalibanta kyautukan ba-zata

Malama ta tafka hatsari, ta rasu tana hanyar kai wa dalibanta kyautukan ba-zata

  • Wata malamar makarantar kasa da firamere ta tafka hatsari, gami da rasa ranta a kan hanyarta na kai wa dalibanta kyautuka bayan lashe jarabawar karshen zangon karatu
  • An gano yadda Ghasoon Najimi ta rasa ranta sanadiyyar mummunan hatsari a birnin Saudi na Samata bayan wani abun hawa ya shiga gabanta
  • Mijinta, wanda ya raba kyautukan da tayi kudurin badawa a makokin ta, ya siffanta ta a matsayin jajirtacciyar malama, mata mai bada kulawa, sannan mahaifiyar mai nuna kauna

Saudi Arabia - Ghasoon Najimi, wata malamar makarantar kasa da firamare wacce ke kan hanyarta ta zuwa makaranta dauke da kyautuka da niyyar ba wa dalibanta bayan sun lashe jarabawar karshen zangon karatu, ta tafka mummunan hatsarin da ya yi sanadin rasa rayuwarta.

Kara karanta wannan

Mafi girman laifi ta yi: Farfesa Maqari ya goyi bayan kashe dalibar da ta zagi Annabi

An samu labarin yadda hatsarin ya auku a birnin Saudi na Samata sanadiyyar shiga gabanta da wani abun hawa ya yi. Masu amfani da kafafan sada zumuntar zamani sun yi jimamin mutuwar.

Malamar makaranta ta rasu tana hanyar kai wa daliban kyautukan ba-zata
Malamar makaranta ta rasu tana hanyar kai wa daliban kyautukan ba-zata. Hoto daga lifeinsaudiarabia.net
Asali: UGC

Mutane da dama daga birnin sun halarci jana'izar ta. Gwamnan Jazan, Prince Muhammad bin Nasir bin AbdulAziz, ya bayyana alhininsa bisa mutuwar da jajirtacciyar kuma hazikar malamar.

Kafin mutuwarta, Ghasoon Najimi mahaifiya ce ga 'ya'ya hudu da cikin na biyar. Ta so bawa dalibanta kyautar ba-zatar da ta shirya, jaridar Life In Saudi Arabia ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A halin yanzu, mijinta ya raba gaba daya kyautukan da ta shirye bayarwa, wanda aka karba yayin makoki. Mijin ya siffanta ta a matsayin jajirtacciyar malama, mata mai bada kulawa, sannan uwa mai nuna kauna.

Jami'an tsaro a kasar Saudi Arabia sun damke mabarata a Masjid Al-Haram

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

A wani labari na daban, jami'ai a kasar Saudi sun yi ram da mazauna da masu karya dokar da aka kama suna bara a Makkah, wadanda suka hada da cikin dukkan manyan masallatai 2 na Annabi, jaridar The Islamic Inforrmation ta ruwaito.

Kamar yadda hukumomin Saudi suka bayyana, an yi ram da wani mazaunin kasar 'dan kasar Indiya a harabar babban masallacin da wani 'dan kasar Morocco a wajen masallacin bayan an kamasu suna bara don su samu tausayawa daga masu bauta.

Haka zalika, Saudi Gazette ta ruwaito cewa, an hada da wani da ya karya doka 'dan kasar Yemen a jerin sunayen wadanda aka kama, wanda ya yi amfani da sandar guragu ya nuna cewa yana da nakasa don ya roki mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel