Obasanjo da Babbar Ƴarsa Sun Yi wa Juna Habaici cikin Dubban Jama'a

Obasanjo da Babbar Ƴarsa Sun Yi wa Juna Habaici cikin Dubban Jama'a

  • Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, da ’yarsa Iyabo sun ba mutane dariya yayin musayar barkwanci a wani taron jama'a
  • Obasanjo ya yi wa ’yarsa habaici bayan ta ce ba ta san shi ba, inda ya danganta hakan da illar amfani da fasahar AI
  • Tsohon shugaban ya kuma soki yadda wasu ƙwararru ke ba Najeriya shawarwarin tattalin arziki ba tare da sanin halin ƙasar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abeokuta, Ogun - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, da ’yarsa mai kama da shi, Sanata Iyabo Obasanjo, sun mayar da wani taron jama'a wajen barkwanci ranar Juma'a.

An gudanar da wannan lamari ne a babban ɗakin taro na ɗakin karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL), da ke Abeokuta, Ogun.

Yar Obasanjo ta yi wa mahaifinta habaici
Diyar tsohon shugaban kasa a Najeriya, Iyabo Obasanjo Hoto: Iyabo Obasanjo.
Source: UGC

Taron na cikin shirin Ajibosin Platform, wani taron shekara-shekara da ake shirya wa domin bikin al'adun Odun Omo Olowu, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi: Shugaban FUT Minna na farko kuma basarake ya riga mu gidan gaskiya

Habaici da Iyabo ta yi ga Obasanjo

Lokacin da mai jagorantar taron, Farfesa Yemi Oke, SAN, ya ba Iyabo dama ta bayyana ra'ayinta, ta fara da gaishe da manyan baƙi.

Ta ambaci Olowu na masarautar Owu, Oba Saka Matemilola; tsohuwar ministar masana'antu, Mrs Onipeko Akande, da mahaifinta.

Sai dai Iyabo ta ƙare gaisuwarta da ambaton tsohon shugaban ƙasar, Obasanjo, wanda ta ce ba ta san shi ba.

Wannan furuci nata ya sa mahalarta taron fashewa da dariya duba da cewa shi ne mahaifinta.

Jim kaɗan bayan haka, Obasanjo ya karɓi makirufo domin ya ba da gudunmawa kan batun tattaunawar, amma ya fara da yi wa ’yarsa habaici.

Tsohon shugaban ƙasar ya amince cewa ba shi da cikakken sani kan fasahar AI, inda ya yi gargaɗin cewa duk abin da mutum ba zai iya sarrafawa ba, ana iya amfani da shi ta hanyar da ba ta dace ba.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Dan Atiku ya faɗi dalilin fanɗarewa ubansa, ya ɗauki alƙawari ga Tinubu

“Duk abin da ba ya ƙarƙashin ikonka, ana iya amfani da shi wajen cutar da kai.”

Yayin da yake yi wa Iyabo habaici, Obasanjo ya ƙara da cewa:

“Kuma za ku iya ganin an riga an fara amfani da ita ta wannan hanyar, Iyabo ba ta san mahaifinta ba, wannan ma ya nuna an fara amfani da AI ta hanyar da ba ta dace ba.”

Da yake kallon Iyabo, Obasanjo ya ƙara da cewa:

“Wasu daga cikin ’ya'yana, ciki har da Iyabo, sun halarci waɗannan jami'o'i.”

Ya ce Iyabo ma ta yi karatu a ɗaya daga cikin jami'o'in Ivy League, amma ya tambayi yadda za ta gaya masa yadda zai tafiyar da gidansa.

A baya, an ruwaito cewa Obasanjo da ’yarsa sun sake haɗuwa bayan sun samu saɓani a fili sakamakon wata wasiƙa mai zafi da Iyabo ta rubuta wa mahaifinta.

Obasanjo da yarsa sun rikita taro
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo. Hoto: @OluObasanjo.
Source: UGC

Zargin rashin jituwa tsakanin Iyabo da Obasanjo

A wata hira da tashar TVC kwanan nan, Iyabo ta yi watsi da rade-radin cewa akwai saɓani tsakaninta da mahaifinta.

Kara karanta wannan

"Kamar yana raye," Abubuwan da aka ji mabiyan Sheikh Masussuka na fada a wurin jana'iza

Ta bayyana cewa dangantakarsu tana da ƙarfi, kuma ta wuce yadda ake fahimtar alaƙar uba da ’ya.

Tsohuwar sanatar ta ce dangantakarsu ta sauya tsawon shekaru, inda abota ta zama muhimmin ɓangare na rayuwarsu.

Ta ce:

“Ni ce babbar ’ya mace, ban ma san yadda zan bayyana dangantakarmu ba. A yanzu mun fi abokai.
“Zan cika shekara 60 a shekara mai zuwa, shi kuma zai cika shekara 90. A wannan lokaci ba na buƙatar kulawar uba sosai, mun fi zama abokai masu alaƙa mai zurfi.”

Iyabo Obasanjo ta fice daga APC

An ji cewa Sanata Iyabo Obasanjo ta sanar da ficewarta daga APC tana mai zargin shugabannin jam’iyyar da nuna mata rashin mutunci da rashin adalci.

Tsohuwar 'yar majalisar dattawan ta soki tsarin sulhu da ya bai wa Sanata Solomon Adeola tikitin gwamna ba tare da an wani tuntube ta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.