INEC Ta Yi Magana kan Cire Sunan Gwarzo daga Jerin 'Yan Takarar Gwamnan Kano
- INEC ta ce ta tantance tare da amincewa da takarar Abdulsalam Gwarzo na NDC a zaben gwamnan Kano na 2027
- Hukumar ta bayyana cewa umarnin kotun tarayya da ke Kano na ranar 27 ga Oktoba ne ya hana ta wallafa sunan Gwarzo da mataimakinsa
- INEC ta amince da korafe-korafe 66, ta kuma yi watsi da wasu 64 da suka shafi ‘yan takarar gwamna da majalisun dokokin jihohi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa ba ta da wata matsala da takarar dan takarar gwamnan Jihar Kano na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Abdulsalam Gwarzo.
Hukumar ta ce dalilin da ya sa ba a ga sunan Gwarzo a sabon jerin sunayen ‘yan takarar zaben 2027 da ta fitar ba shi ne umarnin kotu, ba wai ta ki amincewa da takararsa ba.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta fara biyan tallafin N50,000 duk wata ga 'yan Najeriya, an ji masu amfana

Source: Twitter
Wani babban jami'in INEC ne ya bayyana hakan ga jaridar Daily Trust, inda ya ce hukumar ta tantance Gwarzo tare da amincewa da takararsa, amma ba za ta iya wallafa sunansa ba har sai an samu hukuncin karshe kan umarnin kotu.
Dalilin da ya sa INEC ba ta wallafa sunan Gwarzo ba
Jami'in ya bayyana cewa kotun tarayya da ke Kano ce ta bayar da wani umarnin wucin gadi a ranar 27 ga Oktoba, wanda ya hana INEC wallafa sunayen ‘yan takarar NDC.
A cewarsa, wannan umarni ne kawai ya hana hukumar saka sunan Gwarzo a jerin ‘yan takarar gwamna da mataimakansu.
Jami'in ya ce:
"Na yi tsammanin na fada muku cewa an tantance shi kuma an amince da takararsa, sai dai ana jiran hukuncin karshe kan wani umarnin wucin gadi da kotun tarayya da ke Kano ta bayar a ranar 27 ga Oktoba, wanda ya hana mu wallafa sunan duk wani dan takarar NDC.
"A takaice dai, ba mu da wata matsala da shi." In ji shi.
Ba Gwarzo da mataimakinsa a jerin INEC
Wannan karin haske ya zo ne bayan an gudanar da bincike a ranar Asabar, 31 ga watan Oktoban 2026 inda aka gano cewa har yanzu ba a saka sunayen Abdulsalam Gwarzo da mataimakinsa, Rabiu Mustapha, cikin sabon jerin sunayen ‘yan takarar gwamna da mataimakansu ba.
A jerin sunayen, INEC ta rubuta kalmar "umarnin kotu" a wuraren da ya kamata a saka sunayen ‘yan takarar gwamna da mataimakinsa na jam'iyyar NDC a Kano.
Wannan mataki ya haifar da tambayoyi kan dalilin da ya sa sunan Gwarzo bai bayyana ba, duk da cewa hukumar ta taba bayyana cewa ta amince da takararsa.
Sai dai bayanin jami'in ya nuna cewa rashin sunan dan takarar a jerin ba yana nufin an soke ko an ki amincewa da takararsa ba.

Source: Facebook
Gwarzo ya yi magana kan cire sunansa
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar gwamnan jihar Kano na NDC, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya ce jam'iyyarsu ta kara farin jini da yawan magoya baya.
Gwarzo ya ce cire sunansa daga jerin ’yan takarar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da farko, ya ƙara wa jam’iyyar farin jini tare da jawo mata ƙarin magoya baya gabanin zaben Kano na 2027.
Asali: Legit.ng
