Gwamna Dauda Lawal Ya Mika Sandar Mulki ga Sabon Sarkin Gusau da Wasu Sarakuna 18

Gwamna Dauda Lawal Ya Mika Sandar Mulki ga Sabon Sarkin Gusau da Wasu Sarakuna 18

  • Gwamna Dauda Lawal ya miƙa sandar mulki ga Sarkin Gusau na 16, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello II, tare da wasu sarakuna 18 a Zamfara
  • Gwamnan ya buƙaci sarakunan gargajiya su haɗa kai da gwamnati wajen dawo da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa
  • Sabon Sarkin Gusau ya yi alƙawarin kafa shugabanci nagari, inganta tsaro da haɗin kan al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa sandar sarauta ga Sarkin Gusau na 16, Mai Martaba Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello II, tare da wasu sarakuna masu daraja ta farko 18.

An gudanar da bikin naɗin sarautar cikin annashuwa a cibiyar baje kolin kasuwanci da ke Gusau a yau Asabar, 31 ga watan Oktoba, 2026.

Dauda Lawal
Gwamna Dauda Lawal lokacin da yake mika sandar mulki ga Sarkin Gusau na 16, Mai Martaba Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello II Hoto: Bahsan TV
Source: Facebook

Leadership ta ruwaito cewa dubban al’umma, masu riƙe da sarautun gargajiya, manyan jami’an gwamnati da sauran manyan baƙi daga sassan Arewa maso Yamma sun halarta.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawar da shakkun 'yan Najeriya, ya fadi dalilinsa na runtumo basussuka

Sabon Sarkin Gusau, wanda zuriyar Malam Sambo Dan Ashafa ne, wanda ya kafa masarautar Gusau, an naɗa shi a watan Yuli 2025 bayan rasuwar mahaifinsa, Alhaji Ibrahim Bello, a ranar 25 ga Yuli, 2025, yana da shekaru 71.

Masarautar Gusau, wadda tarihinta ya samo asali daga jihadin ƙarni na 19 na Daular Sakkwato, na ci gaba da kasancewa cibiyar al’adu da siyasa ta Jihar Zamfara.

Lawal ya buƙaci haɗin kan sarakuna

Yayin miƙa sandar sarautar, Gwamna Lawal ya bayyana sabon sarkin a matsayin mutum mai sauƙin kai, tausayi da tawali’u, wanda yake da ƙwarewar jagoranci.

Ya buƙaci dukkan sarakunan gargajiya a jihar su haɗa kai da gwamnati a kowane mataki domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a Zamfara

“Shugabannin gargajiya su ne masu kula da al’ummarmu da al’adunmu. Dole ne ku kasance fitilu masu haskaka hanyar haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba, tare da bunƙasa zaman tare cikin lumana tsakanin talakawanku da sauran al’umma,” in ji Lawal.

Kara karanta wannan

Matasa sun kira sarki a waya, sun yi barazanar yin garkuwa da shi a Kano

Sarki ya yi alƙawarin shugabanci nagari

A nasa jawabin, Sarkin Gusau, Mai Martaba Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello II, ya yi alƙawarin samar da shugabanci nagari da zai inganta zaman lafiya, tsaro da ci gaba.

Ya tabbatar wa al’ummar masarautar cewa zai tsaya tare da su, ya ƙarfafa haɗin kai tare da jawo ayyukan ci gaba zuwa masarautar.

Sarakuna.
Wasu daga cikin sarakuna 18 da suka karbi sandar mulki daga mai girma gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Hoto: Bahsan TV
Source: Facebook

Haka kuma, ya buƙaci jama’a su kasance masu bin doka da oda tare da goyon bayan manufofin gwamnati.

Kafin babban bikin naɗin sarautar, an gudanar da lacca kan tarihin Malam Sambo Dan Ashafa, wanda ya kafa garin Gusau, da kuma rayuwarsa.

Gwamnan Kebbi ya kirkiro masarautu

Kun ji cewa gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da ƙirƙirar sababbin gundumomi bakwai tare da naɗa hakimai da dagatai a wasu yankunan Masarautar Zuru.

Kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu ya ce an gudanar da naɗe-naɗen bisa dokar ƙananan hukumomin Jihar Kebbi ta 2008

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262