Sanata Yari Ya Fadi Abubuwa 3 da Za Su ba Tinubu Nasara a Zaben 2027
- Abdulaziz Yari ya ce imanin Tinubu ga Allah, ayyukansa da kuma kokarin kwamitin yakin neman zaben APC za su taimaka masa wajen samun nasara a 2027
- Yari ya bayyana hakan ne a Makkah, Saudiyya, lokacin da ya raka Shugaba Tinubu da wasu manyan ‘yan Najeriya aikin Umrah
- Tsohon gwamnan Zamfara ya ce APC za ta yi amfani da ayyukan da ta gudanar wajen gamsar da ‘yan Najeriya su sake zaben Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Makkah, Saudiyya - Shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC (APC-PCC), Sanata Abdulaziz Yari, ya bayyana dalilan da ya sa yake ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sake lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2027.
Yari ya ce imanin Tinubu ga Allah, ayyukan da yake gudanarwa a matsayinsa na shugaban kasa da kuma karfin kwamitin yakin neman zaben APC na gamsar da al'umma za su taimaka wajen samun nasararsa.

Source: Twitter
Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Makkah da ke kasar Saudiyya, inda ya raka Shugaba Tinubu da wasu manyan ‘yan Najeriya gudanar da aikin Umrah, cewar rahoton The Punch.
Abin da Yari ya ce zai taimaka wa Tinubu
Yari ya bayyana cewa imanin Shugaba Tinubu ga Allah da addu'o'in da yake yi wa Najeriya na daga cikin abubuwan da suka ba shi kwarin gwiwar cewa shugaban zai samu nasara a zaben 2027.
Ya ce yayin da suke gudanar da aikin Umrah a kasa mai tsarki, Tinubu ya fara da yin addu'a ga Najeriya da daukacin al'ummarta kafin ya yi magana kan makomar zaben shugaban kasa.
Tsohon gwamnan ya ce:
"Wannan shi ne abin da ke nuna jagoranci, domin idan ka tambaye shi, abin da ya fara yi shi ne addu'a ga kasa, ya yi addu'a ga kowane dan Najeriya.
"Ya kuma ce wannan zabe Allah ne ya riga ya zabi wanda zai zama shugaba, domin Allah ne kadai ke iya dora mutum a kan mulki ko kuma hana shi."
APC za ta yi yakin neman zabe
Sanata Yari ya kara da cewa nasarar Tinubu a zaben 2027 ta dogara ne ga ikon Allah, kamar yadda ya bayyana cewa Allah ne ya taimaka masa ya lashe zaben 2023, jaridar Leadership ta kawo labarin.
Sai dai ya jaddada cewa hakan ba zai hana jam'iyyar APC gudanar da ayyukan yakin neman zabe da suka dace ba domin gamsar da al'umma.
A cewarsa, wajibi ne mambobin kwamitin yakin neman zaben su tattauna da jama'a, su bayyana manufofin gwamnati da kuma ayyukan da ta gudanar domin neman goyon bayansu.
"Don haka, komai yana hannun Allah, ya yi masa yadda ya yi masa a shekarar 2023. Amma Allah ya umurce mu da mu yi kokari, mu gudanar da dukkan matakan da suka dace wajen yakin neman zabe, tattaunawa da mutane, gamsar da su da kuma nuna musu abin da muka yi da nasarorin da muka samu." In ji shi.
Yari ya kara da cewa yana da yakinin cewa da yardar Allah, ‘yan Najeriya za su gamsu da kokarin APC tare da sake zaben Tinubu.

Source: Facebook
Makiyaya sun gode wa Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Kungiyoyin makiyaya daga sassa daban-daban na Najeriya sun nuna godiyarsu ga Shugaba Bola Tinubu bisa kafa Ma’aikatar Raya Kiwo ta Tarayya.
Sun kuma yi alƙawarin ci gaba da goyon bayan sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa domin bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
Asali: Legit.ng


