Karo na 2 a cikin sati 1, sojin Najeriya sun dakile 'yan ta'ddan ISWAP daga jefa bama-bamai a Maiduguri

Karo na 2 a cikin sati 1, sojin Najeriya sun dakile 'yan ta'ddan ISWAP daga jefa bama-bamai a Maiduguri

  • A karo na biyu, dakarun sojin kasan Najeriya sunyi nasarar dakile harin 'yan ta'addan da sukayi kokarin aukawa Maiduguri, ana saura kwanaki watan Ramadana ya kare
  • Dakarun sojin kasan Najeriya sunyi luguden wutar ne yayin da sukayi ido biyu da wasu 'yan bindigan da ake zargin mayakan ISWAP ne a daji kusa da wajen gari
  • Wata majiya daga rundunar ta bayyana yadda sojin suka bude wa 'yan bindigan wuta, yayin da suka shirye dasa abubuwa masu fashewa cikin garin Maiduguri

Borno - A karo na biyu a jere, dakarun sojin kasan Najeriya sun yi nasarar dakile harin 'yan ta'addan daga shiga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ana saura kwanaki watan Ramadana ya kare.

'Yan ta'addan da ake zargin mayakan ISWAP ne, sun yi yunkurin aukawa Maiduguri a daren Laraba, misalin 11:50 daga yankin Polo, amma dakarun sojin kasan Najeriya suka tarwatsasu ta hanyar amfani da manyan makamai wajen harar 'yan ta'addan da suka hango a cikin daji kusa da wajen garin.

Kara karanta wannan

Shakku da tantama ta shiga zukatan jama'a kan sojan da ke aiki da ISWAP kuma ya halaka kansa

Karo na 2 a cikin sati 1, sojin Najeriya sun dakile 'yan ta'ddan ISWAP daga jefa bama-bamai a Maiduguri
Karo na 2 a cikin sati 1, sojin Najeriya sun dakile 'yan ta'ddan ISWAP daga jefa bama-bamai a Maiduguri. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC
"Dakarun sojin sun hango 'yan ta'addan cikin daji, inda suka gansu da tarin yawa suna kai komo daga yankin bishiyoyin kashu wajen Polo, hakan yasa sojin bude musu wuta.
"Wata majiya mai karfi ta bayyana yadda 'yan ta'addan suka shirya jefa abubuwa masu fashewa cikin garin Maiduguri. Sai dai a yayin da aka hango su, sojin suka yi hanzarin tarwatsasu.
"Duk karararrakin da ku ke ji daga jami'an sojin ne, babu harsashi daya da 'yan ta'addan suka harba," wani jami'in kungiyar hadin guiwa ya tabbatar wa Punch.

Haka zalika, da safiyar Juma'a, dakarun sojin kasan Najeriya sun ragargaji 'yan Boko Haram, yayin da suka kai wani hari a tsakiyar dare a Gajiram, karamar hukumar Nganzai dake jihar Borno.

Bayanin da aka samu daga rundunar sojin cikin Gajiram ya bayyana yadda dakarun suka ragargaji 'yan ta'addan, tare da gudunmawar sojin sama na Operation Hadin Kai.

Kara karanta wannan

Hotuna: Sojin Najeriya sun ragargaji Boko Haram, sun halaka Amir da shugaban malaman 'yan ta'addan

"Dakarunmu sun musu luguden wuta. Hakan yasa suka gudu, gami da tserewa ta yankin Gudumbali tare da gudunmawar dakarun sojin saman Najeriya.
"Cikin hanzari aka turo da jiragen yakin sama don bada gudunmawa ga sojin kasan, wadanda ke tsaka da luguden wuta ga 'yan ta'addan," majiya daga rundunar ta bayyana.

Gajiram ita ce hedkwatar karamar hukumar Nganzai, wacce za ta kai misan 73km daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Hotuna: Sojin Najeriya sun ragargaji Boko Haram, sun halaka Amir da shugaban malaman 'yan ta'addan

A wani labari na daban, labari mai dadi da ke zuwa daga rundunar sojin Najeriya shi ne na nasarar da suka samu a samamen da suka kai karkashin Operation Desert Sanity.

Zakakuran sojojin Najeriyan sun samu nasarar halaka mayakan ta'addanci na Boko Haram da ISWAP da ke yankin Manjo Ali Qere a jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Afirilun 2022 inda sojojin suka sheke Amir da wani shugaban malaman 'yan ta'addan na Galta a samamen.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ƴan Siyasan Najeriya Sun Fi Boko Haram Hatsari, In Ji SSANU

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng