Shakku da tantama ta shiga zukatan jama'a kan sojan da ke aiki da ISWAP kuma ya halaka kansa

Shakku da tantama ta shiga zukatan jama'a kan sojan da ke aiki da ISWAP kuma ya halaka kansa

  • Akwai shakku kan yadda mai bada umarni a rundunar sojin Najeriya ya halaka kansa bayan gano yana hada kai da Boko Haram din da suka kai hari anguwanni a Yobe
  • Haka zalika, wata gamsassar majiya ta tabbatar da yadda Jibrin ya ambaci sunayen wasu daga cikin abokan aikinsa, wadanda a halin yanzu suke fuskantar tuhuma
  • Sai dai, wani kwamandan sojin ruwan Najeriya ya ce a ganin wasu daga cikinsu, hana shi magana aka yi don gudun allura ta tono garma

Akwai shakku game da rahoton yadda mai bada umarni a rundunar sojin Najeriya na Geidam dake jihar Yobe, Lance Corporal Jibrin, wanda aka kama bayan gano yadda yake hadai kai da 'yan ta'addan Boko Haram, wadanda suka kai hari yankunan Yobe cikin kwanakin nan ya halaka kansa.

Kara karanta wannan

An damke sojan da ke hada kai da ISWAP, ya bindige kansa ana shirin mika shi bariki

An gano yadda Jibrin, wanda ya yi batan dabo daga wurin aikinsa na wasu kwanaki da suka wuce, ya koma cikin 'yan ta'addan Boko Haram din da suka kai hari anguwan Geidam a makon da ya gabata.

Shakku da tantama ta shiga zukatan jama'a kan sojan da ke aiki d ISWAP kuma ya halaka kansa
Shakku da tantama ta shiga zukatan jama'a kan sojan da ke aiki d ISWAP kuma ya halaka kansa. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Majiyoyi daga rundunar sojin sun bayyana yadda sashin binciken sirrin sojin kasan suka bibiyi sojan, inda aka gan shi a Gashua, kimanin 100 kilomita daga wurin aikinsa, a ranar Talata.

Majiya mai karfi ta tabbatarwa Daily Trust yadda wanda ake zargin ya ambaci sunan wasu daga cikin abokan aikinsa a matsayin wadanda ke hada kai wajen ta'addanci, inda a halin yanzu suke fuskantar tuhuma.

Sai dai labarai sun zakulo yadda sojan yayin maida shi Geidam ya kwace bindiga daga daya daga cikin wadanda suka tasa keyarsa, tare da fin karfin dayan, sannan ya halaka kansa.

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya kan sabuwar wakar sukar gwamnatin Buhari da Rarara ya yi

"Sanda aka sa mishi ankwa, ana tuhumarsa, ya bayyana wasu sirrika da dama da suka yi sanadiyyar damko wasu daga cikin abokan harkallarsa.
"Yayin maidoshi zuwa Geidam, Jibrin ya kwace bindiga daga daya daga cikin wadanda suka tasa keyarsa, gami da fin karfin dayan sannan ya halaka kansa," kamar yadda rohoton ya bayyana.

Kakakin rundunar sojin kasan yanki na biyu na Operation Hadin Kai Damaturu, Lt Kennedy Anyewau, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

"Eh, mun samu rahoto a kan yadda wani soja ya halaka kansa jiya da yamma, sannan ana cigaba da bincikar lamarin don gano dalilan da suka janyo hakan. Iya abunda zan iya bayyanawa kenan game da lamarin a yanzu," yace.

Yayin zantawa ta waya da Daily Trust, wani kwamandan sojin ruwan Najeriya mai ritaya, Abiodun Durowaiye-Herberts, ya ce akwai abubuwa da dama a kan halaka kan shi da ya yi.

A ganinshi, an hana marigayin magana ne don gudun kada ya fallasa sunayen abokan harkallarsa.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: kwamishinan gwamna Zulum ya yi murabus, zai tsaya takara kujerar yankinsu

Durowaiye-Herberts ya ce, "A ganin wasu daga cikinmu, mun san yadda abubuwa ke wakana. Dole a ce wannan dan gida ne, idan har zai rayu dole allura za ta tono garma, saboda dole ya bayyana sunaye, abunda yafi kawai shi ne a hana shi magana.
"Saboda haka, akwai abubuwa da dama da bamu sani a kan abubuwan da muke kokarin ganowa."

Wani Jami'i wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya yi fashin baki ga Daily Trust game da yadda Jami'in sojan ya hakala kansa.

Ya ce, "Da gaske an kama Jibrin, sannan daga baya ya halaka kansa. Soja ne wanda ya san kan aikinsa sosai; a da yana cikinmu, amma daga lokacin da ya gano ana zarginsa, ya yi batan dabo.
"Babbu shakka harin da 'yan Boko Haram suka kai Geidam na karshe ya bamu matukar mamaki, saboda mun shirya kai musu farmaki, amma suka daukemu ba-zata ta hanyar amfani da wani sabon salon da ba mu san su da shi. Sun sadada cikin anguwan ba tare da ababen hawa ba, kuma ba karar harbin bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun yi ikirarin alhakin halaka 'yan sanda 3 a Kogi

"Sai da mu ka yi zargin akwai mai kai musu labari a cikinmu, amma bayan tsananin bincike aka gano Jibrin ne."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: