Gwamnatin Katsina Ta FadiGa Gaskiyar Abin da Ya Faru da Aka Kona Motocin APC a Kamfe

Gwamnatin Katsina Ta FadiGa Gaskiyar Abin da Ya Faru da Aka Kona Motocin APC a Kamfe

  • Gwamnatin Katsina ta ce rikicin Yankara ya samo asali ne daga rashin jituwa tsakanin masu Mauludi da jami’an tsaro kan hanyar da za su bi
  • Gwamnatin ta musanta cewa lamarin yana da alaka da gangamin yakin neman zaben Gwamna Dikko Radda da Shugaba Bola Tinubu a Faskari
  • Gwamnatin ta bukaci jami’an tsaro su gudanar da bincike, tare da gargadin kafafen yada labarai kan yada bayanan da ba a tantance ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Gwamnatin Jihar Katsina ta yi karin haske kan rikicin da ya faru a garin Yankara da ke karamar hukumar Faskari.

Gwamnatin ta bayyana cewa lamarin ba shi da alaka da gangamin yakin neman zaben Gwamna Malam Dikko Umaru Radda.

An yi gangamin APC a Katsina
Gwamna Dikko Radda na jawabi da taron magoya bayan APC Hoto: Ibrahim Kaula Mohammed II
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Asabar, 31 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan

"Ka cika alkawari"; Basarake ya yi wa Gwamna Radda albishir

Gwamnatin ta bayyana cewa rahotannin da ake yadawa a kafafen sada zumunta da ke alakanta rikicin da gangamin yakin neman zaben gwamnan ba su yi daidai da bayanan farko da ta samu ba.

A cikin sanarwar, gwamnatin ta ce rikicin ya samo asali ne daga rashin jituwa tsakanin mahalarta jerin Mauludi da jami’an tsaro.

Abin da ya haddasa rikicin Yankara

Sanarwar ta bayyana cewa bayanan farko sun nuna cewa an samu sabani ne tsakanin masu gudanar da Mauludi da jami’an tsaro kan hanyoyin da aka ware domin gudanar da muzaharar.

Hakan ya haifar da rudani a wani titin jama'a da ke cikin garin Yankara, amma gwamnatin ta jaddada cewa lamarin bai da alaka da ayyukan yakin neman zaben gwamnan ko gangamin Tinubu-Dikko da aka gudanar a Faskari.

Yadda Dikko Radda ya isa Faskari

Gwamnatin ta bayyana cewa Gwamna Dikko Radda ya bi ta garin Yankara cikin kwanciyar hankali yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Faskari domin gudanar da ayyukan da suka hada da gangamin yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara biyan tallafin N50,000 duk wata ga 'yan Najeriya, an ji masu amfana

Ta ce da isar gwamnan Faskari, ya fara ziyartar fadar hakimi, inda Hakimin Faskari da sauran shugabannin gargajiya suka tarbe shi.

Daga nan ne gwamnan ya wuce sakatariyar karamar hukumar Faskari, inda ya duba ayyukan gyaran da ake gudanarwa a ginin sakatariyar da kuma zauren taron majalisar karamar hukumar.

Bayan kammala duba ayyukan, Gwamna Radda ya halarci gangamin yakin neman zaben tare da ganawa da mazauna yankin da magoya bayansa.

Gwamnati ta bukaci a gudanar da bincike

Gwamnatin Katsina ta bukaci hukumomin tsaro da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma yanayin da rikicin ya biyo baya.

Haka kuma, ta yi kira ga kafafen yada labarai, masu rubutun ra'ayin yanar gizo da masu amfani da kafafen sada zumunta da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa ko yadawa.

Gwamnatin ta ce yada bayanan da ba a tantance ba, musamman wadanda za su iya haifar da rudani da kara tayar da hankali, na iya jefa al'umma cikin tashin hankali.

Kara karanta wannan

"Mun cika alƙawura": Radda ya nemi Katsinawa su sake bashi dama a 2027

A karshe, gwamnatin ta bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankulansu, su kiyaye zaman lafiya tare da gujewa yada rahotannin da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.

Radda ya je Faskari
Gwamna Dikko Radda a wajen kamfe a Faskari Hoto: Ibrahim Kaula Mohammed II
Source: Facebook

Gwamna Radda ya samu yabo

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Yamman Katsina kuma Hakimin Faskari, Engr. Alhaji Aminu Tukur Usman Sa’ad, ya yabawa Gwamna Malam Dikko Umaru Radda.

Hakimin na Faskari ya yaba wa Gwamna Radda ne bisa cika alkawuran da gwamnatinsa ta dauka ga al’ummar Karamar Hukumar Faskari lokacin yakin neman zaben kakar da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng