Tinubu Ta Ƙaddamar da Yadda ’Yan Najeriya Za Su Iya Neman Rance Ta Waya

Tinubu Ta Ƙaddamar da Yadda ’Yan Najeriya Za Su Iya Neman Rance Ta Waya

  • Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin SPARK wanda zai bai wa ’yan Najeriya damar neman rance ta wayoyin salula ba tare da amfani da intanet ko wayoyin zamani ba
  • Shirin zai taimaka wa masu neman rance a karon farko da masu ƙaramin kuɗin shiga su fara gina tarihin karɓa da biyan bashi
  • CREDICORP ta ce ta taimaka wajen samar da rance sama da Naira biliyan 53.5 ga ’yan Najeriya 351,000 tun bayan fara ayyukanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon shirin bayar da rance mai suna SPARK, wanda zai bai wa ’yan Najeriya damar neman rance ta wayoyin salula ba tare da buƙatar wayar zamani ko intanet ba.

Shirin wanda CREDICORP ta samar, zai yi amfani da fasahar USSD domin sauƙaƙa wa jama'a samun damar karɓar rance.

An tsara shirin ne musamman domin taimaka wa mutanen da ba su taɓa karɓar rance a hukumance ba, masu ƙaramin kuɗin shiga da kuma waɗanda ba sa iya samun damar amfani da tsarin rance na bankuna.

Kara karanta wannan

Abba Hikima ya fito da abin da ya kamata mutane su sani kan takarar Pantami da Aminu Gwarzo

A cewar CREDICORP, ana sa ran shirin zai fara samun karɓuwa sosai a tsakanin ’yan Najeriya kafin ƙarshen shekarar 2026.

Tinubu ya kawo hanyar bai wa 'yan Najeriya bashi cikin sauki
Yadda aka kaddamar da shirin Spark | Hoto: CREDICORP
Source: Facebook

Yadda za a nemi rancen SPARK

Ba kamar sauran manhajojin bayar da rance da ke buƙatar wayar zamani da haɗin intanet ba, SPARK zai yi aiki ne ta hanyar fasahar USSD.

Wannan na nufin mutanen da ke amfani da wayoyin hannu na yau da kullum za su iya fara neman rance ba tare da sauke wata manhaja ko amfani da intanet ba.

Hukumar CREDICORP ta bayyana cewa mutanen da suka karɓi rance kuma suka biya shi a kan lokaci za su iya gina ingantaccen tarihin karɓar bashi.

Wannan tarihin zai iya taimaka musu samun damar wasu manyan rance da sauran hidimomin kuɗi a nan gaba.

Sai dai har yanzu hukumar ba ta bayyana lambar USSD da za a yi amfani da ita ba, adadin kuɗin da mutum zai iya karɓa, kuɗin ruwa ko cikakkun sharuddan cancanta ba.

An ƙaddamar da shirin a Jihar Abia

An gabatar da shirin SPARK a lokacin wani taron CREDICORP for All da aka gudanar a Aba, Jihar Abia, inda fiye da mutane 1,000 suka samu bayanai kan hanyoyin samun rance.

Kara karanta wannan

Matasa sun shiga babbar matsala da suka jefi magoya bayan APC a tawagar gwamna

Taron ya haɗa da masu ciniki, cibiyoyin kuɗi, masana'antun cikin gida da wakilan gwamnati.

An kuma gudanar da baje kolin hanyoyin samun rance ga mata masu sana'o'i, matasa da masu harkokin sufuri.

Haka kuma, an nuna babura masu ƙafa uku da aka haɗa a Najeriya waɗanda ake samar wa mutane ta hanyar tsarin rance na CREDICORP mai suna S.C.A.L.E.

Shirin na da manufar haɗa masu buƙatar kayayyaki da masana'antun cikin gida ta hanyar samar da sauƙaƙan rance.

Gwamnatin Abia ta yi alƙawarin tallafi

Da yake wakiltar Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, Chinenye Mba-Uzoukwu ya bayyana cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin samar da yanayin da zai taimaka wa harkokin kasuwanci da zuba jari.

Ya ce inganta harkokin kasuwanci zai taimaka wajen sauƙaƙa wa ’yan kasuwa, matasa da iyalai samun damar rance.

Shi ma Armstrong Ume Takang, Manajan Darakta na MOFI kuma mamba a kwamitin gudanarwar CREDICORP, ya bayyana shirin a matsayin hanyar mayar da manufofin gwamnati zuwa damarmakin tattalin arziki ga jama'a.

CREDICORP ta taimaka wa mutum 351,000

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta sauya salo, ta amince da wani tsari da talakawa za su amfana a Najeriya

Babban Daraktan CREDICORP, Uzoma Nwagba, ya ce manufar hukumar ita ce faɗaɗa damar samun rance fiye da tsarin da bankuna suka saba amfani da shi.

Ya bayyana cewa hukumar ta taimaka wajen samar da rance sama da Naira biliyan 53.5 ga ’yan Najeriya fiye da 351,000 tun bayan fara ayyukanta.

A cewarsa, mata sun kai kusan 59% na waɗanda suka amfana da rancen, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng