Yan Bindiga sama da 30 Sun Bakunci Lahira yayin da Suka Yi Yunƙurin Kai Hari a Jihar Zamfara
- ’Yan sanda sun ce an gano gawarwaki sama da 30 da ake zargin na ’yan bindiga ne a gonaki da ke kusa da garin Bukuyum, jihar Zamfara
- Hakan ya biyo bayan arangama tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga da suka yi ƙoƙarin kai hari garin
- Rundunar ’yan sandan ta ce ba a tantance ainihin adadin waɗanda suka mutu ba, domin ’yan bindiga kan kwashe gawarwaki da waɗanda suka ji rauni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - An gano gawarwaki sama da 30 da ake zargin na ’yan bindiga ne a gonaki da ke kewaye da garin Bukuyum a Jihar Zamfara.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da hakan, ta ce an gano gawarwakin ne bayan arangama tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga da suka yi yunkurin kai hari.

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta ce jami’anta, tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron sa-kai na yankin, sun dakile yunƙurin kai hari garin Bukuyum.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, ya ce aikin ya fara ne a ranar 28 ga Disamba, 2026, bayan da wasu ’yan bindiga suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin garin.
A cewar rundunar, jami’an tsaro sun yi musayar wuta mai zafi da maharan, inda suka hana su kutsawa cikin garin.
An gano gawarwakin yan bindiga
Rundunar ta ce daga bisani an gano gawarwaki sama da 30 a gonakin da ke kewaye da garin, waɗanda ake kyautata zaton na ’yan bindigar da aka kashe ne. Wannan na nuna cewa maharan sun yi asarar rayuka masu yawa.
Sai dai, ’yan sandan sun ce har yanzu ba a tabbatar da ainihin adadin waɗanda suka mutu ba, saboda ’yan bindiga kan kwashe gawarwakin waɗanda suka mutu da kuma waɗanda suka ji rauni daga wuraren da aka yi faɗa.
Rundunar ta bayyana cewa nasarar kare garin ta hana yiwuwar asarar rayuka, lalata dukiyoyi da kuma sake raba mazauna yankin da muhallansu.
An ƙara matsin lamba kan ’yan bindiga
Sanarwar ta ƙara da cewa binciken farko kan yanayin tsaro ya nuna cewa ci gaba da matsin lambar sojoji da sauran jami’an tsaro ya tilasta wa wasu daga cikin ’yan bindigar da suka rage barin jihar.

Source: Original
Rundunar ’yan sandan ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da gudanar da samamen fatattakar ’yan bindiga tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki, domin kawar da miyagu a yankin.
Ta ce ayyukan na da nufin dawo da amincewar jama’a ga hukumomin tsaro da kuma tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin mazauna al’ummomin da abin ya shafa.
Sojoji sun gano bama-bamai a Zamfara
Kun ji cewa dakarun sojoni sun gano tare da lalata bama-bamai da 'yan ta'adda suka dasa a hanyar Magami-Hannutara-Dansadau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Dakarun sun dauki matakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan abubuwan fashewar da aka dasa domin haddasa babbar barna ga matafiya da sauran masu amfani da hanyar.
Asali: Legit.ng

