Zaben 2027: Barau Jibrin Ya Ce Duk Alamu Na Nuna Tinubu Zai Yi Nasara a Zaɓe
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya ce duk alamu na nuna Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaɓen 2027
- Barau ya yi wannan hasashen ne yayin ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓen APC a ƙananan hukumomi uku na Jihar Kano
- Ya buƙaci ’yan jam’iyyar APC su haɗa kai su yi aiki domin samun nasarar ’yan takarar jam’iyyar a zaɓen mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kano - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Barau ya ce nazarin da manazarta siyasa suka yi da kuma yadda siyasar Najeriya take a halin yanzu na nuna cewa Tinubu zai sake samun nasara a zaɓen mai zuwa, rahoton Punch.
Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓe na ƙananan hukumomin Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado a Jihar Kano.

Kara karanta wannan
"Dogaro ga Allah SWT da wasu abubuwa 2 da za su taimaki Shugaba Tinubu a zaɓen 2027"
A wajen taron, Barau ya buƙaci mambobin jam’iyyar APC su haɗa kai tare da yin aiki domin ganin dukkan ’yan takarar jam’iyyar sun samu nasara a babban zaɓen 2027.

Source: Twitter
Barau Ya Yabi Gwamnatin Tinubu
A cewar wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya fitar, Barau ya ce matakan da Tinubu ya ɗauka a zangon mulkinsa na farko za su haifar da sakamako mai kyau a zangonsa na biyu.
Ya ce:
“Bisa nazarin da manazarta siyasa suka yi da kuma halin da siyasar Najeriya take ciki a yanzu, dukkan alamu na nuna cewa, da yardar Allah, Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaɓen shugaban ƙasa.”
Mataimakin shugaban majalisar ya kuma yaba wa shugabannin APC, waɗanda aka zaɓa da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke bai wa jam’iyyar.
Ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa haɗin kan APC a Kano zai ci gaba da ƙarfafa jam’iyyar.
Barau Ya Yi Magana kan Kano
Barau ya bayyana Kano a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da suka fi yawan masu rajistar zaɓe a Najeriya, inda ya ce jihar ce ta biyu bayan Legas.
Ya ce saboda yawan masu zaɓe da muhimmancin jihar, Kano ta cancanci kulawa ta musamman da kuma samun damar cin moriyar ayyukan raya ƙasa daga Gwamnatin Tarayya.
Ya kuma bayyana sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC a matsayin matakin siyasa da ya ƙara wa Kano muhimmanci.
A cewarsa, haɗin kan gwamnan da shugabannin ƙananan hukumomi, kansiloli, ’yan majalisar jiha da na tarayya a ƙarƙashin APC zai taimaka wajen samar da ci gaba ga al’ummar jihar.
Ya Buƙaci A Fara Gangamin Zaɓe
Barau ya ce kafa kwamitocin yaƙin neman zaɓen na da manufar haɗa shugabannin jam’iyya, tsofaffi da sabbin ’yan majalisa, kansiloli da sauran manyan jiga-jigai.
Ya buƙaci mambobin kwamitocin su fara wayar da kan masu zaɓe tare da gudanar da gangamin neman goyon baya ga ’yan takarar APC.
Sanatan ya ce zaɓen mai zuwa dama ce ga waɗanda aka zaɓa su ƙara ba da gudummawa wajen ci gaban al'ummomin da suke wakilta.
Asali: Legit.ng
