Jami'an tsaron Saudiyya sun cafke 'yan Pakistan 150 da suka yi ihun take siyasa a Masjid Annabawi

Jami'an tsaron Saudiyya sun cafke 'yan Pakistan 150 da suka yi ihun take siyasa a Masjid Annabawi

  • Jami'an Saudi sun yi ram da wasu 'yan Pakistan 150 bayan sun yi kirari ga wanda suke goyon baya, tare da amfani da kalmomin cin zarafi ga abokan hamayyarsu na siyasa
  • Wasu 'yan gwagwarmayar kasa Pakistan sun shiga hannu, an yanke musu hukuncin shekaru 5 a gidan yari, cin su tarar SR60,000, tare da haramta musu Hajji da Umara har abada
  • Sai dai, ana sa ran zane wadanda suka yi amfani da kalmomin batancin, tare da hukuncin zaman gidan yari har karshen rayuwarsu bayan tsananta bincike da aka yi

Saudi Arabia - Hukumomin Saudi sun yi ram da wasu 'yan siyasan kasa Pakistan (PTI), wadanda suka karya dokar masallacin Annabi mai tsarki, gami da shirya musu hukunci mai tsanani.

Kara karanta wannan

Kalaman Sarkin Waka: Mun yi dawafi a kanka, mun hada ka da Allah, Jarumai maza a Saudiyya

An kama mutane 150, tare da yanke musu hukuncin shekaru biyar a gidan yari, cinsu tarar 60,000 riyal, gami da haramta musu aikin Hajji da Umrah na har abada saboda cin mutunci a cikin masallacin Annabi.

Jami'an tsaron Saudiyya sun cafke 'yan Pakistan 150 da suka yi ihun take siyasa a Masjid Annabawi
Jami'an tsaron Saudiyya sun cafke 'yan Pakistan 150 da suka yi ihun take siyasa a Masjid Annabawi. Hoto daga islamicinformation.com
Asali: UGC

The Islamic Information ta rahoto cewa, ana sa ran nadawa wadanda suka yi kirarin ko sukayi amfani da kalmomin cin zarafin duka, tare da daurin rai da rai a gidan yari bayan tsananta bincike da aka yi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da za a sanar da masu bada shaidan damar yin Umara da Hajji na Pakistan ba da jimawa ba, sannan dokokin za su tsananta.

Wani bidiyo ya yi yawo a kafafan sada zumuntar zamani, wanda ya nuna yadda dandazon jama'a ke fatattakar wata tawagar gwamnati, gami da kiraye-kirayen da babu da'a ko ladabi a ciki.

Hukumomin Saudi sun yi ram da Sahibzada Jahangir wanda aka fi sa ni da Chico da sauran abokansa uku da Imran Khan, bayan an gano yadda suka yi kiraye-kirayen kamfen din siyasa, tare da hada kai wajen cin zarafi duk a cikin masallacin Annabi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan Shi'a da jamian tsaro sun yi arangama, soji sun harbi mutum 8 a Zaria

Magoya bayan PTI sun yi kirari a masallacin Annabi bayan isowar abokan hamayyar siyasa a daren da ya gaba, tare da rigima da ma'aikatan gwamnati. Gwamnatin Saudi ta kama wadanda ke da alhakin.

Hajj 2022: Saudi Arabia ta kayyade shekarun mahajjata, duk wanda ya wuce 65 bashi da rabo bana

A wani labari na daban, a ranar Asabar, Ma'aikatar Hajji da Umara ta Saudi Arabiya ta sanar da makurar shekaru 65 ga mahajjatan da zasu yi aikin Hajjin wannan shekarar. Ma'aikatar ta dakatar da wadanda suka shigar da bukatar yin aikin Hajji da suka kai shekaru 65 kafin watan Afirilu.

Sa dokar Hajjin za ta zama alkhairi ga wadanda basu kai shekaru 65 ba. Hukuncin zai shafi mahajjatan da suka wuce shekaru 65, da kuma wadanda suka shigar da bukatar su da dattawa, mata ko tare da iyayensu a matsayin Muharramansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel