Georgina Rodriguez ta na samun £80, 000 wajen Ronaldo a kowane wata

Georgina Rodriguez ta na samun £80, 000 wajen Ronaldo a kowane wata

Rade-radi na yawo cewa a duk wata Tauraron ‘Dan kwallon Duniya Cristiano Ronaldo ya kan ba Sahibarsa watau Georgina Rodriguez makudan dalolin kudi.

Cristiano Ronaldo shi ne ‘Dan kwallon da ya fi kowa samun kudi a halin yanzu. Wannan ya sa Georgina Rodriguez mai shekara 26 a Duniya ta ke morewarta.

An fahimci cewa a kowane wata Misis Georgina Rodriguez ta kan tashi da fam £80, 000 daga hannun Masoyin na ta domin ta rika daukar dawainiyar kanta.

Rodriguez ce ta haifawa Ronaldo ‘Diya Alana Martina wanda ta ke da shekaru biyu yanzu a Duniya. An haifi Alana Martina dos Santos Aveiro ne a 2017.

Bayan haka Georgina Rodriguez ce ke kula da sauran ‘Ya ‘yan Ronaldo uku duk da ba ita ta haife su ba. Daga cikinsu akwai wasu Tagwaye da aka haifa masa.

KU KARANTA: Sura da irin zubin Ronaldo ta sa na ke kaunarsa - Georgina Rodriguez

Georgina Rodriguez ta na samun £80, 000 wajen Ronaldo a kowane wata
Sahibar Ronaldo ta na tashi da miliyoyin kudi ban da sana'arta
Asali: Getty Images

Haka zalika Misis Georgina Rodriguez ce tamkar Mahaifiyar babban ‘Dan Ronaldo watau Cristiano Ronaldo Jr. wanda aka haifa a cikin Watan Yunin shekarar 2010.

Jaridar Corriere dello ta ce Ronaldo ya kan ba Masoyiyar ta sa wannan kudi ne domin ta rika kula da kanta. Ana sa ran cewa nan gaba kadan Masoyan za su yi aure.

Idan aka yi lissafin wannan kudi da Georgina Rodriguez ta ke samu a hannun ‘Dan wasan, za su haura Naira miliyan 30 a kudin gida, a shekara fiye da Miliyan 300.

A lokacin da tsohon ‘Dan wasan na Real Madrid da Manchester United, Ronaldo, ya cika shekaru 35 a Duniya, Georgina Rodriguez ta saya masa wata gangariyar mota.

Rodriguez ta ba Cristiano Ronaldo mamaki a wajen bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kyautar katuwar motar marsandi kirar G-Wagon ta kusan Miliyan 250.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel