Ronaldo Ya Ce Ya Fi Kowa Iya Kwallo a Tarihin Duniya, Ya Fadi Dalilin Rashin Zuwansa Barce

Ronaldo Ya Ce Ya Fi Kowa Iya Kwallo a Tarihin Duniya, Ya Fadi Dalilin Rashin Zuwansa Barce

  • Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa ya kusa rattaba hannu a Barcelona a baya kafin ya koma Manchester United
  • Fitaccen ɗan wasan na kasar Portugal ya ce shi ne ya fi kowa iya taka leda a tarihin wasan kwallon kafa a duniya
  • Ronaldo ya ce darajojin da ya samu a rayuwarsa a wasan kwallo sun tabbatar da cewa shi ne mafi kwarewa a tarihi
  • Wani mai goyon bayan Barcelona, Muhammad Sa'idu ya ce yana da ja a kan ikirarin da Cristiano Ronalda ya yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Madrid, Spain - Fitaccen ɗan wasan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bayyana yadda ya kusa komawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona kafin ya kammala cinikin da ya kai shi Man United.

A wata hira, Ronaldo ya nuna cewa ya yi imani da cewa shi ne gwarzon ɗan wasan kwallon kafa a tarihin wasannin duniya.

Kara karanta wannan

Dan tsohon gwamna, Bello ya fadi matsayarsa kan rigimar El Rufai da Uba Sani da ake yi

Ronald
Ronaldo ya ce ya fi kowa iya kwallo a duniya. Hoto: Cristiano Ronaldo
Asali: Getty Images

Ronaldo, wanda ke buga wa Al Nassr ta Saudiyya wasa a halin yanzu, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin talabijin na La Sexta na kasar Spain.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ronaldo: "Ni ne gwarzon dan kwallon duniya"

Cristiano Ronaldo, wanda zai cika shekara 40 a duniya a ranar Laraba, ya yi fariyar cewa babu wanda ya taɓa kai matsayin da ya kai a wasan kwallon kafa.

"Ina ganin ni ne gwarzon ɗan wasan kwallon kafa da ya taɓa wanzuwa a tarihin wasa. Babu wanda ya fi ni.
Rawar da na taka a lokuta da dama na tabbatar da hakan,"

- Cristiano Ronaldo

Ya ƙara da cewa mutane na iya son Lionel Messi, Diego Maradona ko kuma Pele, amma ba wanda ya kai shi a cikinsu.

Dan kwallon ya ce:

"Na ga mutane da dama suna jin daɗin kallon Messi ko Maradona ko Pele, kuma ina girmama hakan, amma ni ne mafi cikakken ɗan kwallon da ya taɓa kasancewa.

Kara karanta wannan

Marcelo: Shahararren tsohon dan wasan Real Madrid ya yi ritaya daga buga kwallon kafa

"Nasarorin da na samu a tarihi sun isa su tabbatar da hakan,"

Yadda Ronaldo ya kusa zuwa Barcelona

A cikin hirar, Ronaldo ya tabbatar da cewa kungiyar Barcelona ta yi ƙoƙarin daukar sa lokacin da yake buga wasa a Sporting Lisbon, kafin Manchester United ta shigo cikin cinikin.

"Da zan koma buga wasa a Barcelona. Sun yi ƙoƙarin saye na a lokacin da nake a Sporting Lisbon.
"Sun nuna sha'awar su, amma shekara guda bayan haka Manchester United ta zo ta saye ni,"

Wannan bayani ya sanya tambayoyi da dama daga masoya kwallon kafa, musamman ganin irin muhawara mai zafi da ke tsakanin masoya Ronaldo da Lionel Messi.

Fitattun abubuwan da Ronaldo ya cimma

Cristiano Ronaldo ya buga wa manyan kungiyoyi kamar Sporting Lisbon, Manchester United, Real Madrid, Juventus da Al Nassr wasa a cikin rayuwarsa ta kwallon kafa.

Kara karanta wannan

'Na bambanta da su': Buhari ya fadi halin da abokansa na yarinta da karatu ke ciki

Ya ci kyautar Ballon d’Or sau biyar tare da cin kofuna da dama a matakin kulob da na kasa da kasa.

Fabrizio Romano ya rahoto cewa Ronaldo ya ci kwallaye sama da 920 a wasannin da ya buga a gasar kwallon kafa ta duniya.

"Ina da ƙarfi, ina da sauri, kuma zan iya zura kwallo da kai ko kuma da kafa ta hagu. Babu wani da ya fi ni kamala a dukkanin waɗannan fannoni.
"Ni ne mafi girma a tarihin wasan kwallon kafa,"

- Ronaldo

Legit ta tattauna da Muhammad Sa'idu

Wani mai goyon bayan Barcelona, Muhammad Sa'idu ya ce ba kamshin gaskiya a cikin maganar da Ranaldo ya yi.

"Ai Hausawa sun ce duk wanda ya ce shi ne, to ba shi ba ne. Fitowa fili ya ce ya fi kowa ma ya nuna bai fi kowa ba.
Haka idan aka lura kan yadda bai taba cin kofin duniya ba za a gane har yanzu da sauransa a harkar kwallon kafa."

Kara karanta wannan

"Su na cewa maulidi bidi'a ne," Sarkin Kano ya yi raddi a kan 'Qur'an convention'

- Muhammad Sa'idu

Victor Osimhen zai koma Juventus

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kwallon kafa ta Juventus na shirin kashe €75m domin sayen dan wasan Najeriya, Victor Osimhen.

A yanzu haka Victor Osimhen na tsakiyar shuhurarsa a kungiyar kwallon Galatasaray, inda ya zura kwallaye da dama a kakar wasa ta bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng