An Kama Mai Shiga Makabarta Yana Cire Likkafani a Jikin Gawar da aka Birne
- Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta kama wani mutum mai shekaru 30 bisa zargin haƙa kabari a makabartar Machika da ke Ribah
- Wanda ake zargin mai suna Tapro Tareza, mazaunin ƙauyen Changu da ke gundumar Kanya, ana zarginsa da lalata kaburbura tare da cire wasu abubuwa daga gawa
- Rundunar ta ce an kama shi ne bayan matasan yankin sun cafke shi yana haƙa sabon kabari, sannan suka sanar da ’yan sanda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Birnin Kebbi – Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta sanar da kama wani mutum mai shekaru 30, mai suna Tapro Tareza, bisa zargin haƙa kabari a makabartar Machika da ke yankin Ribah.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Bashir Usman, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 24 ga Nuwamba, 2026.

Source: Facebook
Bashir ya wallafa a Facebook cewa an kama wanda ake zargin ne bayan samun rahotannin lalata kaburbura a makabartar, lamarin da ya sa ’yan sanda suka haɗa kai da matasan yankin domin sanya ido kan wurin.
Yadda aka kama wanda ake zargin
Sanarwar ta ce a ranar 10 ga Nuwamba, 2026, da misalin ƙarfe 7:15 na yamma, jim kaɗan bayan birne wani mamaci, aka ga wanda ake zargin yana haƙa kabarinsa.
Matasan yankin ne suka cafke shi tare da sanar da ’yan sanda, waɗanda suka karɓe shi domin gudanar da bincike.
Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa kama shi ya biyo bayan ƙoƙarin da aka yi na gano mutumin da ke lalata kaburbura a makabartar.
Abin da binciken farko ya gano
SP Bashir Usman ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa wanda ake zargin na cire wasu abubuwa daga jikin mamata.
Ya kuma ce wanda ake zargin ya amsa cewa yana da hannu a wasu ayyukan lalata kaburbura da aka aikata a makabartar a baya.
Sanarwar ta ƙara da cewa ya amsa hannu a wani lamari da ya shafi cire likkafanin wani mamaci tare da tafiya da shi.

Source: Original
'Yan sanda sun fara zurfafa bincike
Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike domin gano cikakken abin da ya faru da kuma tabbatar da cewa wanda ake zargin ya fuskanci matakin shari’a da ya dace.
'Yan sanda sun yaba da sa ido da haɗin kan al’ummar yankin, amma ta gargaɗi jama’a da kada su ɗauki doka a hannunsu.
Sun buƙaci mazauna jihar da su riƙa sanar da jami’an tsaro duk wani motsi da suke zargi, ta hanyar kiran lambobin 09039911876 ko 07081974395.
An kashe 'yan NDC a Delta
A wani labarin, kun ji cewa rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane shida tare da jikkatar wasu da dama a rikicin da ya ɓarke yayin wani gangamin siyasa a jihar Delta.
Lamarin ya faru ne a al’ummar Uduere da ke ƙaramar hukumar Ughelli North, inda tawagar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ta zargi wasu ’yan bindiga da kai musu hari.
Rundunar ’yan sanda ta ce ta fara bincike domin gano ainihin adadin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata, tare da gano waɗanda suka haddasa rikicin.
Asali: Legit.ng

